DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeBabban Labari Hadi Sirika ya nuna jirgin Ethiopian Airlines a matsayin Nigeria Air -...

Hadi Sirika ya nuna jirgin Ethiopian Airlines a matsayin Nigeria Air – Shaida a gaban kotu 

Kotun Abuja Babban Birnin Tarayyar Nijeriya ta saurari shaidar mai gabatar da kara na 12, Christopher Odofin, wanda ya bayyana cewa tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, ya yi amfani da jirgin Ethiopian Airlines da aka sanya wa tambarin Nigeria Air domin nuna cewa an kaddamar da kamfanin jirgin na kasa kafin karshen gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

A sakamakon zaman kotun da hukumar EFCC ta wallafa a shafinsa na Facebook, ta ce shaidar ya ce an kawo jirgin Abuja ne a ranar 27 ga Mayu, 2023 domin nuna wa jama’a na tsawon kasa da kwanaki uku, kafin a mayar da shi Addis Ababa a ranar 29 ga Mayu, ranar mika mulki.

Odofin ya kuma shaida wa kotun cewa binciken EFCC ya gano an kulla yarjejeniya da Ethiopian Airlines ne kwanaki biyar kacal kafin Sirika ya bar ofis, inda aka shirya amfani da ma’aikatan jirgin na Ethiopian Airlines da kuma wasu mutane sanye da kayan Nigeria Air domin daukar hotuna.

Ya kara da cewa an kuma tsawaita kwangilar aikin kafa Nigeria Air ga kamfanin Tianaero Nigeria Limited daga sama da N299m zuwa fiye da N599m bisa umarnin Sirika. Alkalin kotun, Mai Shari’a S.C. Oriji, ya dage sauraron karar zuwa ranar 17 ga Yuni, 2026 domin ci gaba da shari’ar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata