Nijeriya da Saudiyya sun bayyana aniyar ƙara faɗaɗa haɗin gwiwarsu a fannonin noma, makamashi, zuba jari, sufurin jiragen sama, fasahar kuɗi da kasuwanci.
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin wani taron liyafar bikin cikar Saudiyya shekaru 96 da samun ‘yancin kai.
Gidan talabijin na TVC News ya ruwaito Idris ya ce alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu, wadda ta samo asali daga tarihi, addini da hulɗar al’umma, yanzu tana ƙara samun sabon salo na tattalin arziki da dabarun haɗin gwiwa.
Ya ce Najeriya na da damar koyon darussa daga yadda Saudiyya ta samu ci gaba, yayin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki karkashin manufar Renewed Hope.
Ministan ya ce gwamnatin tarayya na zuba jari a hanyoyi layin dogo, inganta samar da wutar lantarki da sake fasalin ɓangaren mai da iskar gas, tare da ƙara mai da hankali kan noma, masana’antu, fasahar zamani da harkar nishaɗi.
Ya kuma gayyaci ’yan kasuwa da masu zuba jari daga Saudiyya su ƙara duba damar da ke akwai a Nijeriya, musamman a noma da samar da abinci, makamashi, ababen more rayuwa, ma’adinai da fasaha.
A cewarsa, ƙasashen biyu za su iya ƙara ƙarfafa dangantakarsu ta hanyar bunƙasa kasuwanci, zuba jari, musayar ƙwarewa da ƙulla sabbin yarjejeniyoyin haɗin gwiwa.
