DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, April 21, 2026
HomeKetareNijar na neman haɗin gwiwa don magance matsalar tsaro a yankin Sahel...

Nijar na neman haɗin gwiwa don magance matsalar tsaro a yankin Sahel da Afirka

Ministan harkokin wajen Nijar, Bakary Yaou Sangaré, ya halarci taro a birnin Dakar karo na 10 kan samar da zaman lafiya da tsaro a Afirka da aka gudanar a birnin Dakar.

A jawabin da ya gabatar, ya jaddada buƙatar fahimtar matsalolin tsaro da ke addabar yankin Sahel da ma Afirka baki ɗaya, yana mai cewa tsoma bakin ƙasashen waje da gasa tsakanin ƙasashe na daga cikin abubuwan da ke dagula zaman lafiya.

Ya kuma yi Allah-wadai da tasirin irin waɗannan tsoma baki da kuma wasu tsare-tsaren yankuna da ke taimakawa wajen tsawaita rikice-rikicen tsaro.

Dangane da batun ta’addanci, ministan ya ce an dade ana zargin wasu ɓangarori da bayar da tallafi ko nuna halin ko-in-kula ga ƙungiyoyin ‘yan ta’adda, yana mai kira da a gudanar da bincike mai zurfi, gaskiya da kuma sahihanci kan lamarin.

Ya ƙara da cewa ƙasashen Afirka sun zama kamar suna fuskantar matsala ne sakamakon arzikin da suke da shi, inda ake amfani da wannan arziki wajen haddasa rikice-rikice.

A ƙarshe, Nijar ta bukaci ƙasashen Afirka su haɗa kai tare da farfaɗo da tattaunawa mai zurfi, domin gina aminci tsakanin ƙasashe da kuma samar da mafita mai dorewa da ‘yancin kai ga nahiyar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata