DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, May 13, 2026
HomeKetareNijeriya za ta kwaso 'yan kasar da suka maƙale a Afrika ta...

Nijeriya za ta kwaso ‘yan kasar da suka maƙale a Afrika ta Kudu

Gwamnatin Nijeriya ta fara shirye-shiryen kwashe ’yan kasar da ke zaune a ƙasar Afirka ta Kudu, inda akalla mutum 130 suka riga suka yi rajista domin komawa gida bisa radin kansu, sakamakon karuwar hare-hare da kalaman ƙiyayya ga baki a ƙasar.

Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa wannan mataki na zuwa ne bayan sake barkewar zanga-zanga da kalaman ƙiyayya ga ’yan ƙasashen waje a wasu sassan Afirka ta Kudu, musamman a biranen Pretoria da Johannesburg.

Zanga-zangar dai na da nasaba da zargin da ake yi wa bakin haure kan matsalolin tattalin arziki, rashin aikin yi da kuma matsalar tsaro da ƙasar ke fuskanta, lamarin da ya haddasa fargaba a tsakanin ’yan Nijeriya da ke zaune a can.

Ministar Harkokin Wajen Nijeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, ta bayyana a ranar Lahadi cewa kare lafiyar ’yan Nijeriya a ƙasashen waje shi ne babban fifiko ga gwamn6ati, don haka aka fara tattara bayanan waɗanda ke son dawowa gida domin shirya musu jiragen dawowa.

Ta ƙara da cewa, ya zuwa yanzu mutum 130 sun yi rajista tare da ofishin jakadancin Nijeriya da ke Afirka ta Kudu, kuma ana sa ran adadin zai ƙaru, yayin da ƙungiyoyin ’yan Nijeriya a ƙasar ke taimakawa wajen wannan tsari.

Ministar ta kuma nuna damuwa kan yadda ake samun ƙaruwar zanga-zangar nuna ƙiyayya ga baki, inda ta ce Shugaba Tinubu, ya nuna matuƙar damuwa tare da kira ga hukumomin tsaro na ƙasar da su ɗauki matakan da suka dace.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata