Sanatan da ke wakiltar yankin Gombe ta Tsakiya, Muhammad Danjuma Goje, ya yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta hanyar “consensus” da jam’iyyar APC a jihar Gombe ta ɗauka.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa shugabannin jam’iyyar sun amince da DCP Mohammed Ahmadu Deba (mai ritaya) a matsayin ɗan takarar APC na kujera da Goje ke riƙe da ita, a wani taro da aka gudanar ranar Lahadi ƙarƙashin jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya.
Sai dai a wata sanarwa da hadiminsa kan harkokin shari’a, Barrista Saidu Mu’azu Kumo, ya fitar, Sanata Goje — wanda ke neman wa’adi na biyar a Majalisar Dattawa — ya ce taron “consensus” ɗin bai haɗa da dukkan ‘yan takarar da aka tantance ba, domin ya shafi Gwamna Yahaya ne kawai tare da wasu kaɗan daga cikin masu neman takarar.
