DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeSiyasaPeter Obi ya bukaci Tinubu ya yi murabus bisa zargin gaza magance...

Peter Obi ya bukaci Tinubu ya yi murabus bisa zargin gaza magance matsalolin Nijeriya

Dan takarar shugabancin Nijeriyaa jam’iyyarNDC, Peter Obi ya bukaci Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi murabus daga mukaminsa, yana mai danganta bukatar da tabarbarewar tattalin arziki, matsalar tsaro da kuma abin da ya kira gazawar gwamnati wajen gudanar da mulki.

Jaridar Punch ta ruwaito Obi ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X bayan ya yi tsokaci kan sanarwar da Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, ya yi na shirinsa na yin murabus daga mukaminsa.

A cewar Obi, murabus din Starmer ya nuna yadda shugabanni a kasashen da suka ci gaba ke daukar alhakin gazawar gwamnatinsu idan suka kasa cika alkawuran da suka dauka wa al’umma.

Ya ce kafin zaben shekarar 2015, Tinubu ya kasance cikin wadanda suka rika kira ga tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, da ya yi murabus saboda matsalolin tsaro da tattalin arziki, musamman bayan sace daliban Chibok.

Obi ya tunatar da alkawuran da Tinubu ya yi a lokacin yakin neman zaben 2023, ciki har da samar da ingantaccen wutar lantarki, yaki da cin hanci da rashawa, inganta tsaro da kuma kyautata rayuwar ‘yan Najeriya.

Sai dai ya ce bayan shekaru uku na mulkin Tinubu, wadannan alkawura ba su cika ba. A cewarsa, matsalar rashin wutar lantarki na ci gaba da addabar kasar, matsalar garkuwa da mutane ta karu, yayin da tsadar rayuwa da wahalhalun tattalin arziki suka tsananta.

Obi ya kara da cewa wasu bangarori kamar samar da ababen more rayuwa, sufuri, tsaro da yaki da cin hanci da rashawa sun kara tabarbarewa maimakon samun ci gaba.

A karshe, ya ce yana hada kai da ‘yan Najeriya masu kishin kasa wajen kira ga shugaban kasar da ya yi murabus domin tabbatar da al’adun rikon amana da daukar alhakin shugabanci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata