DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeSiyasaGwamnatin Kano ta rufe kwalejojin koyon harkokin lafiya biyu

Gwamnatin Kano ta rufe kwalejojin koyon harkokin lafiya biyu

Gwamnatin jihar Kano ta rufe wasu kwalejojin koyon harkokin lafiya guda biyu da ke karamar hukumar Nasarawa bisa zargin karya doka, ƙa’idojin aiki da kuma rashin cika sharuddan gudanar da irin waɗannan makarantu.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ma’aikatar lafiya ta jihar Kano, Nabilusi Abubakar K/Na’isa, ya fitar.

Sanarwar ta ce an ɗauki matakin ne bayan bincike da tantancewa da ya nuna cewa makarantun suna gudanar da ayyukansu ba tare da izini ba.

Makarantun sun haɗa da IBN SINA College of Health Science and Technology da ke Dakata Kawaji kusa da Masallacin Juma’a, da kuma Life Line College of Health Science and Technology da ke Dakata Industrial Area, Bela Road, Tsamiyar Gare, kan titin Mai Sikeli.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata