DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, October 2, 2026
HomeWasanniPortugal ta rasa mabiya Instagram sama da miliyan 1.4 cikin sa’o’i 24...

Portugal ta rasa mabiya Instagram sama da miliyan 1.4 cikin sa’o’i 24 kan rikicin Ronaldo da mai horas da tawagar

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Portugal ta rasa sama da mabiya miliyan 1.4 a shafinta na Instagram cikin sa’o’i 24, yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan rikicin da ya kunno kai tsakanin kyaftin ɗin ƙasar, Cristiano Ronaldo, da koci Jorge Jesus.

Wani bincike da Jaridar Daily Trust ta gudanar a safiyar Juma’a ya nuna cewa yawan mabiya shafin ƙungiyar ya ragu daga kusan miliyan 24.9 zuwa miliyan 23.5.

Raguwar mabiyan ta zo ne bayan Ronaldo ya bar sansanin horas da ‘yan wasan Portugal da ke Denmark, sakamakon rashin jituwa da kocin ƙungiyar, Jorge Jesus.

Rahotanni sun ce Ronaldo ya bar sansanin ne ranar Laraba bayan ganawa da shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Portugal, Pedro Proença, kafin daga bisani ya tabbatar da tafiyarsa a wani saƙo da ya wallafa a Instagram.

Rikicin ya samo asali ne bayan Jesus ya yanke shawarar ajiye Ronaldo a benci a wasan da za a fara, lamarin da ya ƙara dagula rashin jituwar bayan kocin ya yi magana a bainar jama’a kan batun.

Kafofin yaɗa labaran Portugal ma sun ruwaito raguwar mabiya shafin ƙasar, inda A Bola ta ce sama da mutum 300,000 sun daina bin shafin cikin ƙasa da sa’o’i 24, yayin da Renascença, bisa bayanan HypeAuditor, ta ce adadin ya ragu zuwa 24,631,902.

A halin yanzu, Ronaldo na ci gaba da kasancewa cikin mutanen da suka fi yawan mabiya a Instagram, inda binciken shafinsa a ranar Juma’a ya nuna yana da kusan mabiya miliyan 679.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata