DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Thursday, October 1, 2026
HomeSiyasaZaben 2027 ne zakaran gwajin dimokuraɗiyyar Nijeriya - Jonathan

Zaben 2027 ne zakaran gwajin dimokuraɗiyyar Nijeriya – Jonathan

Tsohon Shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan, ya ce babban zaben 2027 zai kasance wani gwaji ga girman dimokuraɗiyyar ƙasar, inda ya bukaci ’yan Nijeriya su fifita zaman lafiya, haɗin kai da adalci.

Jaridar Punch ta ruwaito Jonathan ya bayyana hakan ne a sakonsa na ranar ’yancin kan Nijeriya ranar Alhamis, yayin da ƙasar ke bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kai.

Tsohon shugaban ya bukaci ’yan Nijeriya su ci gaba da nuna kishin ƙasa da jajircewa wajen kare haɗin kan ƙasar, musamman yayin da ake shirin shiga sabon zangon siyasa da za a gudanar da babban zaben 2027.

Ya ce duk da irin ƙalubalen da Nijeriya ta fuskanta tun bayan samun ’yancin kai, al’ummar ƙasar sun ci gaba da shawo kansu ta hanyar juriyarsu, yana mai kira ga ’yan Nijeriya da su kasance masu fata da haɗin kai.

Jonathan ya ce Nijeriya na da dimbin damar samun ci gaba idan aka yi amfani da bambance-bambancen al’ummarta da albarkatun ƙasa da na ɗan Adam wajen samar da ci gaba mai ɗorewa.

Ya kuma yi kira ga matasa da su kasance masu fata da ƙarfin hali, tare da yin aiki tukuru domin gina Nijeriya da za ta samar da kyakkyawar makoma ga al’ummomi masu zuwa.

A cewarsa, samun irin wannan makoma na buƙatar shugabanni a dukkan matakai su nuna ƙarin kishin ƙasa, ɗaukar nauyi da yin mulki nagari.

Kazalika ya kuma buƙaci a magance ƙalubalen zamantakewa da tattalin arziki ta hanyar sadaukarwa, riƙon amana, bin doka da yin aiki domin gina ƙasa mai zaman lafiya, tsaro da adalci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata