Rikici ya ɓarke a jam’iyyar ADC reshen Kano yayin da Ibrahim Khalil da Ibrahim Ali-Amin ke ikirarin mallakar tikitin takarar gwamna na jam’iyyar a zaɓen 2027.
Wasu jiga-jigan ADC a Kano sun ce Ibrahim Khalil ne ya lashe zaɓen fidda gwani da kuri’u 55,851, yayin da Al’amin Little ya samu 4,000.
Jaridar Premium Times ta ruwaito sun yi watsi da duk wani yunƙuri na kakaba wani ɗan takara daga matakin ƙasa.
Sai dai Al’amin Little ya musanta zargin, yana mai cewa har yanzu ana gudanar da tattaunawar sasanci kuma za a mutunta hukuncin ƙarshe na shugabancin jam’iyyar.
Rikicin ya nuna rarrabuwar kai tsakanin shugabannin ADC na Kano da na ƙasa, lamarin da ka iya shafar shirye-shiryen jam’iyyar gabanin zaɓen 2027.
