Jam’iyyar APM ta ce sakamakon zaɓen gwamnan jihar Osun da aka gudanar ranar Asabar ya nuna cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na iya fuskantar shan kaye a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Jaridar Punch ta ruwaito APM ta bayyana cewa nasarar da jam’iyyar adawa ta samu a Osun, jihar da ake ganin tana da muhimmiyar alaƙar siyasa da Tinubu, na nuna cewa masu zaɓe na iya kayar da jam’iyyar da ke mulki idan ba su gamsu da yadda take tafiyar da mulki ba.
A zaɓen, Gwamna Ademola Adeleke na jam’iyyar Accord ya sake lashe zaɓen, inda ya kayar da ɗan takarar APC, Bola Oyebamiji, bayan fafatawa mai zafi.
A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran ƙasa na APM, Yusuf Abubakar, ya fitar ranar Lahadi, jam’iyyar ta ce sakamakon zaɓen ya bayyana raguwar goyon bayan APC da kuma ƙara samun buƙatar sauyin shugabanci a matakin tarayya.
APM ta ce nasarar da Adeleke ya samu a Osun na iya zama wata alama ga abin da zai iya faruwa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, musamman yayin da jam’iyyun siyasa ke fara shirin fafatawar da ke tafe.
Jam’iyyar ta kuma yi iƙirarin cewa yadda wasu magoya bayan APC suka nuna rashin jin daɗinsu ga shugabannin jam’iyyar yayin da suke barin jihar Osun na nuna cewa akwai ƙaruwar rashin gamsuwa da gwamnatin APC.
A cewar APM, matsalolin tattalin arziki, rashin tsaro, rashin aikin yi da abin da ta kira gazawar shugabanci na daga cikin abubuwan da za su iya tasiri kan zaɓen 2027.
Jam’iyyar ta ce mutane da dama na ƙara kallon Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, a matsayin ɗan takarar da ke da kwarewa da tarihin gudanar da mulki wanda zai iya jagorantar ƙasar.
Makinde, wanda ya zama gwamnan Oyo tun shekarar 2019, zai kammala wa’adinsa na biyu a 2027, kuma APM ta ce zai yi takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin tutarta.
APM ta ƙara da cewa Makinde ya nuna ƙwarewar gudanar da harkokin tattalin arziki da siyasa, tana mai danganta ci gaban tattalin arzikin Oyo da salon mulkinsa.
Sai dai jam’iyyar ba ta gabatar da takamaiman hujjoji da za su tabbatar da ikirarin cewa gwamnatin Tinubu ita ce mafi muni a tarihin Nijeriya ba, sai dai ta jero hauhawar farashi, rashin aikin yi, matsalar tsaro da matsalolin tattalin arziki a matsayin abubuwan da take ganin ke ƙara jefa gwamnati cikin suka.
APM ta kuma gargadi APC da kada ta yi tunanin yin magudi a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, tana mai cewa duk wani yunƙurin karkatar da zaɓen daga abin da masu zaɓe suka yanke zai fuskanci turjiya daga al’umma.
Jam’iyyar ta ce sakamakon zaɓen Osun ya ƙara mata ƙwarin gwiwar fafutukar neman nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, inda ta yi alkawarin jagorantar abin da ta kira ƙoƙarin sauya gwamnatin APC.
