DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeSiyasaSanata Shehu Buba ya fice daga APC, ya koma PRP

Sanata Shehu Buba ya fice daga APC, ya koma PRP

Sanata Shehu Buba, ya fice daga jam'iyyar APC

Sanatan da ke wakiltar Bauchi ta Kudu a Majalisar Dattawa, Shehu Buba, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC ya na shirin komawa jam’iyyar PRP, yana mai zargin rashin adalci da kin bin dimokuradiyya a jam’iyyar APC.

A wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai da sadarwa, Sabo Mohammed, ya fitar ranar Lahadi, Sanatan ya bayyana cewa ya dauki matakin ne bayan tattaunawa da magoya bayansa, matasa, mata da masu ruwa da tsaki a siyasance a fadin Bauchi ta Kudu da ma jihar Bauchi baki daya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Shehu Buba, wanda ya taba neman takarar gwamnan Bauchi a karkashin APC kafin daga bisani ya janye daga takarar gabanin zaben fidda gwani, ya ce jam’iyyar ta gaza bai wa mambobi dama da adalci wajen yanke hukunci.

Ya kuma zargi APC da nuna wariya ga mambobin da suka dade suna aiki da jam’iyyar tare da yin watsi da bukatun magoya bayanta a kasa.

Sanatan ya bayyana cewa ya zabi komawa PRP ne saboda akidun jam’iyyar na adalci, gaskiya, rikon amana da shugabanci mai anfani ga talakawa.

Shehu Buba ya kuma bukaci magoya bayansa da sauran abokan siyasarsa su mara masa baya a sabon babin siyasar da ya bude, domin ceto kasar nan daga matsalolin talauci, rashin aikin yi, matsalar tsaro da kuma tabarbarewar tattalin arziki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata