Mai horar da tawagar ƙasar Spain, Luis de la Fuente, ya saka matashin ɗan wasa Lamine Yamal cikin jerin ‘yan wasan da za su wakilci ƙasar a gasar Kofin Duniya ta 2026 duk da rahotannin cewa yana fama da rauni.
Rahotanni sun bayyana cewa Yamal ya samu matsalar rauni a baya-bayan nan, lamarin da ya janyo damuwa tsakanin magoya baya da masu bibiyar ƙwallon ƙafa kan ko zai samu lafiya kafin fara gasar.
Sai dai kocin Spain ɗin ya nuna amincewa da yanayin lafiyar ɗan wasan, yana mai cewa an saka shi cikin tawagar ne bayan amincewar likitoci da jami’an lafiya na ƙungiyar.
