Kungiyar SERAP ta shigar da hukumar zaben Nijeriya INEC kara a gaban kotu, tana zargin hukumar da gaza binciken zargin cewa gwamnoni da aka zaba karkashin jam’iyyar APC sun karkatar da Naira biliyan 800 daga kudaden rabon asusun gwamnatin tarayya FAAC domin harkokin siyasa da yakin neman zabe.
A cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare ya fitar a ranar Lahadi, kungiyar ta ce an shigar da karar a makon da ya gabata a babbar kotun tarayya da ke Abuja, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Da take dogaro da rahotannin kafafen yada labarai, kungiyar ta ce, “Ana zargin gwamnoni na APC da bayar da gudunmawar wata-wata daga kudaden da suke samu na FAAC zuwa wani asusun yakin neman zabe na musamman domin tallafa wa yakin neman sake zaben shugaba Bola Tinubu.”
Kungiyar ta kuma makala wani sharhi da marubuci Festus Adedayo ya wallafa a jaridar Premium Times a ranar 17 ga Mayu, 2026, a matsayin hujja (Exhibit A3) don goyon bayan bukatarta.
Ƙungiyar ta buƙaci INEC ta binciki lamarin, ta bayyana tushen kuɗaɗen da aka tara, tare da tabbatar da cewa dukkan jam’iyyun siyasa suna bin tanade-tanaden dokar zaɓe kan kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe.
SERAP na neman kotu ta bayar da umarnin tilastawa INEC gudanar da bincike kan wadannan zarge-zarge.
