DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeBabban Labari Shugaba Tinubu yace yana ɗora Nijeriya akan turbar da kowane ɗan ƙasa...

Shugaba Tinubu yace yana ɗora Nijeriya akan turbar da kowane ɗan ƙasa zai dara

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce gwamnatinsa na shimfiɗa tubalin sabuwar Najeriya da za ta yi aiki domin ci gaban kowa da kowa tare da bunƙasa tattalin arzikin al’umma baki ɗaya.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin ƙaddamar da aikin tagwayen hanyoyi na Southern Parkway daga Arterial Road S20 (Oladipo Diya Way) zuwa Ring Road II a Abuja. Inda ya samu wakilcin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda.

Ya ce sauye-sauyen da gwamnatinsa ta aiwatar cikin shekaru uku da suka gabata sun kasance masu wahala, amma sun zama wajibi domin ceto tattalin arzikin ƙasa da samar da ci gaba mai ɗorewa.

A cewarsa, sakamakon waɗannan gyare-gyare ya fara bayyana ta hanyar manyan ayyukan more rayuwa da suka haɗa da tituna, gadoji, layukan dogo da gidaje.

Shugaban ya bayyana cewa sabbin hanyoyin suna cikin tsarin babban birnin tarayya na Abuja, kuma idan aka kammala su za su rage cunkoson ababen hawa kuma za su inganta haɗin kai tsakanin sassa daban-daban na birnin.

Ya ce babban titin da aka sanya wa suna Bola Ahmed Tinubu Way tuni ya fara aiki bayan kaddamar da shi, yayin da sabbin tagwayen hanyoyin da aka kaddamar suma za su taimaka wajen sauƙaƙa zirga-zirga ga mazauna yankunan Dutse, Gudu, Gaduwa da Duboyi, waɗanda ke fama da cunkoso musamman a lokutan aiki.

Tun da farko, Mukaddashin Sakataren Hukumar FCDA, Richard Dauda, ya bayyana cewa Southern Parkway na daga cikin manyan hanyoyin da ke haɗa yankunan ci gaban kudancin Abuja, daga Goodluck Jonathan Expressway a Phase I har zuwa Phase IV na babban birnin tarayya.

Ya ce aikin zai taimaka matuƙa wajen inganta sufuri da bunƙasa ci gaban birnin Abuja a nan gaba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata