DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeBabban Labari Sojoji sun yi ajalin ’yan ta’adda tare da tarwatsa su a Neja...

Sojoji sun yi ajalin ’yan ta’adda tare da tarwatsa su a Neja da Kaduna

Rundunar haɗin gwiwa ta Operation FANSAN YAMMA ta sanar da cewa ta samu gagarumar nasara a yaƙin da take yi da ’yan ta’adda da ’yan bindiga, bayan hare-haren sama da ta kai a jihohin Neja da Kaduna, inda aka halaka ‘yan bindiga tare da tarwatsa shirinsu na kai hare-hare.

Rundunar ta ce hare-haren sun gudana ne ranar 29 ga Yuni, 2026, bisa sahihan bayanan sirri da aka samu.

A cewar rundunar, ɗaya daga cikin hare-haren ya auku ne a yankin Dogon Dawa da ke ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja, inda aka gano sama da ’yan ta’adda 200 suna tafiya a kan babura domin kai wani hari.

Rundunar ta ce bayan samun bayanan sirri daga jami’an leƙen asiri da mazauna yankin, jiragen yaƙin sojin saman Nijeriya sun gudanar da sintiri tare da tabbatar da motsin ’yan ta’addan kafin su gano wurin da suka tsaya domin zuba man fetur.

Da aka tabbatar da wurin da suke, jiragen yaƙin sun kai hari ta sama, lamarin da ya yi sanadin halaka ’yan ta’adda da dama, yayin da wasu suka tsere da raunuka zuwa yankin Kurugin Maidawa.

Rundunar ta bayyana cewa harin ya raunana ƙarfin ’yan ta’addan, ya tarwatsa shirinsu tare da hana su kai wasu sabbin hare-hare a yankin Arewa maso Yamma.

A wani samame na daban kuma, rundunar ta kai hari a ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna bayan samun bayanan cewa wasu ’yan bindiga na shirin kai farmaki domin ramuwar gayya kan hare-haren da sojoji suka kai musu a yankin Womba.

A yayin aikin sintirin, jiragen yaƙin sun hango babura uku ɗauke da waɗanda ake zargin ’yan bindiga ne suna kan hanyarsu ta zuwa Dajin Kamuku.

Gidan talabijin na TVC ya ruwaito cewa lokacin da miyagun sun lura da jiragen yaƙin, sun yi ƙoƙarin tserewa, amma sojojin sama sun kai musu hari wanda ya tarwatsa motsinsu tare da dakile shirin da suke yi.

Bayan kammala harin, rundunar ta ce an sake gudanar da bincike tare da haɗin gwiwar sojojin ƙasa, kuma ba a sake gano wata barazana ko motsin ’yan bindiga a yankin ba.

Kwamandan rundunar ya yaba da haɗin gwiwar da ke tsakanin rundunar sojojin sama da ta ƙasa, yana mai cewa irin wannan haɗin kai da amfani da sahihan bayanan sirri ne ke haifar da nasarorin da ake samu a yaƙi da ta’addanci.

Ya kuma tabbatar wa al’ummar yankunan Arewa maso Yamma cewa rundunar za ta ci gaba da kai hare-hare kan sansanonin ’yan ta’adda da ’yan bindiga har sai an kawar da su gaba ɗaya tare da dawo da zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata