DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 21, 2026
HomeKetareSojojin Amurka 624 sun jikkata a yaƙi da Iran

Sojojin Amurka 624 sun jikkata a yaƙi da Iran

Sama da sojojin Amurka 600 ne suka jikkata tun bayan da Amurka ta ƙaddamar da hare-haren soji kan Iran a farkon wannan shekara.

Sabbin alkaluman da Ma’aikatar Tsaron Amurka Pentagon ta fitar sun nuna yadda yaƙin ke ci gaba da jawo asarar rayuka da raunuka, tare da haifar da sabuwar muhawara kan sauye-sauyen da aka yi a bayanan hukumomi na waɗanda aka kashe da waɗanda suka jikkata.

Alkaluman da Ma’aikatar Tsaron Amurka ta fitar, kamar yadda BBC ta ruwaito, ya nuna cewa sojoji 624 sun samu raunuka tun bayan da rikicin ya fara sakamakon umarnin Shugaba Donald Trump na kai hare-hare kan Iran.

Rahoton ya bayyana cewa sojoji 417 daga cikin waɗanda suka jikkata an ƙididdige su ƙarƙashin Operation Epic Fury, sunan da aka ba farmakin farko na Amurka.

Sauran sojoji 207 kuwa an sanya su ƙarƙashin wani sabon rukuni mai suna Overseas Operations.

Sabbin alkaluman sun fito ne duk da cewa Amurka da Iran sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Afrilu, sannan bayan watanni biyu suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna domin kawo ƙarshen rikicin.

Sai dai duk da waɗannan yarjejeniyoyi, kasashen biyu sun ci gaba da zargin juna da karya yarjejeniyar tsagaita wutar, lamarin da ya haddasa sake barkewar hare-haren soji a yankin Gabas ta Tsakiya.

Sai dai Pentagon ta kuma rage adadin waɗanda aka ce sun mutu a ƙarƙashin Operation Epic Fury daga 18 zuwa 14.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata