DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeSiyasaSojojin Nijeriya sun kwato mutane 360 daga hannun ’yan bindiga a Borno

Sojojin Nijeriya sun kwato mutane 360 daga hannun ’yan bindiga a Borno

Rundunar sojin Nijeriya ta ceto mutane 360 daga hannun ’yan bindiga a jihar Borno

Dakarun rundunar Operation Hadin Kai tare da dakaru na musamman sun ceto mutane 360, galibinsu mata da kananan yara, da ’yan ta’adda suka sace daga garin Ngoshe da ke karamar hukumar Gwoza a jihar Borno.

Kwamandan rundunar, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, ya ce an gudanar da samamen ne a yankin tsaunukan Mandara a ranar 6 ga Yuni, inda aka samu nasarar kubutar da wadanda aka sace tun bayan harin da aka kai wa al’ummar Ngoshe a watan Maris.

Sai dai ya ce jarirai biyu sun rasu yayin aikin ceton sakamakon wahalar hanya. An kuma kai wadanda aka ceto asibiti domin kula da lafiyarsu kafin a hada su da iyalansu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata