Daraktar Cibiyar Bincike da Kirkire-kirkire kan Lafiyar Jarirai, Olufunke Bolaji, ta bayyana cewa kusan jarirai 280,000 ne ke mutuwa a Nijeriya duk shekara kafin su samu damar rayuwa da cika burinsu.
Ta ce yawancin mutuwar ana iya kauce mata idan aka inganta kula da mata masu juna biyu da jarirai, da samar da kwararrun ma’aikatan lafiya, ingantaccen tsarin tura marasa lafiya da kuma karfafa cibiyoyin lafiya.
Da yake kaddamar da cibiyar a Ado Ekiti, Gwamnan Jihar Biodun Oyebanji ya ce cibiyar za ta taimaka wajen bincike, horas da ma’aikatan lafiya da samar da sabbin hanyoyin rage mace-macen jarirai a Nijeriya da nahiyar Afirka baki daya.
