DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeLabaraiINEC ta fara bincike kan zargin kutse a bayanan masu zabe

INEC ta fara bincike kan zargin kutse a bayanan masu zabe

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fara bincike kan zargin fallasa bayanan jarumi Emeka Ike, daga rumbun bayanan rajistar masu kaɗa ƙuri’a, tare da zargin amfani da damar shiga shafin hukumar ba bisa ƙa’ida ba.

Lamarin ya samo asali ne bayan Emeka Ike ya yi barazanar ɗaukar matakin shari’a kan mai taimaka wa Ministan Abuja, Nyesom Wike, wato Lere Olayinka, bisa zargin kutse da fallasa bayanansa daga shafin INEC ba tare da izininsa ba.

Kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito, Kwamishinan INEC kuma shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Masu Kaɗa Ƙuri’a, Mohammed Haruna, ya ce binciken ya biyo bayan zargin shiga bayanan tsarin Rajistar Masu Kaɗa Ƙuri’a (CVR) ba tare da izini ba da kuma wallafa bayanan Emeka Ike, wanda ya tsaya takara a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar NDC a Abuja.

INEC ta bayyana lamarin a matsayin mai matuƙar muhimmanci, inda ta ce ta fara cikakken bincike domin gano yadda aka samu damar shiga bayanan. Hukumar ta ce a lokacin aikin rajistar masu kaɗa ƙuri’a, jami’an rajista ne kawai ke samun damar shiga wasu sassan tsarin domin gudanar da ayyukansu, kuma ana cire wannan damar bayan kammala aikin.

A cewar INEC, binciken farko ya gano asusun da aka yi amfani da shi wajen shiga bayanan, kuma an riga an fara tambayar wasu jami’an da abin ya shafa.

Hukumar ta ce tana nazarin dukkan na’urorinta domin gano ko an karya dokokin tsaron bayanai da kuma ɗaukar matakin da ya dace kan duk wanda aka samu da laifi.

Har ila yau, INEC ta ce Hukumar Tsaro ta DSS ma ta fara nata binciken kan lamarin, kuma za ta haɗa kai da hukumomin tsaro wajen tabbatar da an hukunta duk wanda aka samu da hannu a cikin abin da ya faru.

Sai dai hukumar ta jaddada cewa samun bayanan mutum ɗaya ba yana nufin an kutsa cikin dukkan tsarin bayanan masu kaɗa ƙuri’a fiye da miliyan 90 da ke hannunta ba. Ta ce babu wata shaida da ke nuna cewa an samu matsala ga sauran bayanan masu rajista.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata