DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeSiyasaTinubu ne nake goyon baya a 2027, ba APC ba – Wike

Tinubu ne nake goyon baya a 2027, ba APC ba – Wike

Ministan birnin tarayyar Nijeriya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa goyon bayan da yake bai wa shugaban Nijeriya, Bola Tinubu, domin sake zaɓensa a shekarar 2027, bai shafi hana jam’iyyar PDP tsayar da ’yan takara a sauran kujerun zaɓe ba.

Wike ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da babban mataimakinsa na musamman kan hulɗa da jama’a da kafafen sada zumunta, Lere Olayinka, ya fitar ranar Talata, kamar yadda gidan talabijin na TVC News ya ruwaito.

Wike ya ce goyon bayansa ya taƙaita ne ga ƙoƙarin tabbatar da sake zaɓen Tinubu a matsayin shugaban Nijeriya, yayin da PDP ke da ’yancin shiga zaɓukan gwamnonin jihohi, na majalisar dokoki ta kasa da kuma majalisun dokokin jihohi.

Ministan ya ce bai taɓa yi wa kowa alkawarin cewa PDP ba za ta tsayar da ’yan takara a sauran zaɓukan da za a gudanar a 2027 ba.

Ya ce abin da ya yi alkawari shi ne zai tattara masu goyon bayansa domin ganin Tinubu ya samu nasarar komawa kan kujerar shugaban ƙasa a wa’adi na biyu.

Wike ya kuma musanta zargin cewa ƙungiyar kawancen siyasar da ake kira Rainbow Coalition tana da alaƙa da jam’iyyar APC, yana mai cewa ƙungiyar wani dandali ne da wasu ’yan siyasa da jam’iyyu suka kafa domin tallafa wa Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa.

A cewarsa, kungiyar ba a ƙarƙashin APC take ba, illa dai tana ƙoƙarin haɗa masu goyon bayan sake zaɓen Tinubu daga jam’iyyu daban-daban.

Wike ya bayyana cewa tun kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2023, bai taɓa tattaunawa da APC kan wannan matsaya ba, yana mai cewa shi da sauran mambobin ƙungiyar G5 sun goyi bayan Tinubu ne a lokacin zaɓen.

Ya ce matsayinsa na 2027 bai canza ba, domin har yanzu yana da niyyar tattara goyon bayan da zai taimaka wajen ganin Tinubu ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa.

“Abin da na faɗa kuma nake tsayawa a kai shi ne zan tattara masu goyon baya domin sake zaɓen shugaban kasa, ban taɓa yi wa kowa alkawarin cewa PDP ba za ta tsayar da ’yan takara domin gwabza wa a zaɓen gwamna, majalisar dokoki ta kasa da majalisar dokokin jihohi ba,” in ji Wike.

Ministan ya kuma yi watsi da hujjar cewa goyon bayan Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa zai hana masu zaɓe zaɓar ’yan takarar wasu jam’iyyu a zaɓukan jihohi da na majalisun dokoki.

Ya kawo misalin zaɓen 2023 a jihohin Imo, Abia, Enugu da Ebonyi, inda ’yan takarar APC suka samu nasara a wasu kujerun majalisar dattawa duk da cewa Tinubu bai samu kuri’u masu yawa a wasu daga cikin jihohin ba.

Wike ya tambayi yadda APC ta samu kujerun majalisar dattawa biyu a jihar Imo a zaɓen 2023, alhali jam’iyyar ta samu ƙasa da kashi 15 cikin 100 na kuri’un shugaban ƙasa a jihar.

Ya yi amfani da wannan misali wajen nuna cewa masu zaɓe na iya zaɓar ɗan takarar wata jam’iyya a zaɓen shugaban ƙasa, sannan su zaɓi ɗan wata jam’iyya a zaɓen majalisar dokoki ko na gwamnati.

Haka kuma, ya ambaci jihohin Ebonyi, Abia da Enugu, inda ya ce APC ta samu nasarar lashe wasu zaɓukan majalisar dokoki duk da cewa Tinubu bai samu kashi 10 cikin 100 na kuri’un shugaban ƙasa a wasu daga cikin wuraren ba.

Wike ya ce hakan ya nuna cewa masu zaɓe ba lallai ne su zaɓi jam’iyya ɗaya a dukkan matakan zaɓe ba.

Ya ce idan masu zaɓe suka iya zaɓar APC a zaɓen majalisar dattawa a 2023 sannan suka zaɓi wata jam’iyya a zaɓen shugaban ƙasa, babu abin da zai hana su yin irin wannan a 2027 matuƙar suna goyon bayan Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa.

Ministan ya shawarci masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa da su fara mayar da hankali kan sake zaɓen Tinubu kafin su koma fafutukar samun nasara a jihohinsu.

“Bayan an sake zaɓen shugaban kasa, za mu iya komawa mu fuskanci zaɓukan da za a yi a jihohinmu,” in ji shi.

Wike ya kuma ce ba zai ɗauki nauyin taimaka wa ’yan siyasa su samu nasara a zaɓukan da za a yi a jihohinsu ba, yana mai cewa waɗanda ke fuskantar ƙalubalen siyasa ya kamata su warware matsalolinsu a matakin jiha.

Ya jaddada cewa “siyasa ta gida ce”, yana mai gargadin ’yan siyasa da kada su yi amfani da ƙoƙarin sake zaɓen Tinubu wajen tayar da wasu maganganu ko neman samun goyon baya a rikice-rikicen siyasarsu na cikin gida.

A ƙarshe, Wike ya sake jaddada cewa Rainbow Coalition ba wani ɓangare ne na APC ba, sai dai wani dandali ne da ake amfani da shi wajen tattara goyon bayan masu ra’ayin ganin Tinubu ya sake samun wa’adi na biyu.

Ya ce yana ganin Tinubu ya cancanci sake zaɓe saboda abin da ya bayyana a matsayin ayyukan da gwamnatin shugaban ƙasar ta gudanar tun bayan hawanta mulki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata