Tinubu ya bukaci ‘yan Nijeriya su rungumi juriya da hadin kai a bikin babbar Sallah
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci ‘yan Najeriya da su rungumi soyayya, haƙuri da haɗin kai yayin bikin Eid-el-Kabir na bana.
Tinubu ya bayyana hakan ne bayan idar da sallar Idi a Masallacin Dodan Barracks da ke birnin Legas, inda ya ce akwai darussa masu muhimmanci da ya kamata al’umma su koya daga wannan lokaci na ibada da sadaukarwa.
Jaridar Punch ta ruwaito Shugaban ya gode wa Allah da ya ba ‘yan Najeriya damar sake shaida wannan biki, tare da kira ga jama’a da su guji bambancin ƙabila, wariya da ƙiyayya.
Tinubu ya kuma jaddada muhimmancin bin dokokin ƙasa da kuma biyayya ga umarnin Allah domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a cikin al’umma.
Dangane da ma’anar layya kuwa, shugaban ya ce bikin Eid-el-Kabir yana nuna muhimmancin rayuwar ɗan Adam, yana mai cewa Allah ya maye gurbin yanka ɗa da dabba domin nuna darajar rayuwa.
