Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su ci gaba da yi wa ƙasar nan addu’ar samun zaman lafiya, kwanciyar hankali, da cigaba a daidai wannan lokaci da suke shagulgulan Babbar Sallah.
Ministan ya yi kiran ne a cikin saƙon sa na taya ‘yan Nijeriya murnar shagulgulan babbar Sallah.
Ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da jajircewa wajen aiwatar da manufofin inganta rayuwa tare da gina Nijeriya mafi tsaro da wadata, wadda ta rungumi kowa.
Haka kuma, ya shawarci jama’a da su yi amfani da wannan lokaci wajen nuna ƙauna da tallafi ga marasa galihu, inganta zaman lafiya da zaman tare cikin fahimtar juna, da ƙarfafa ruhin haɗin kan ƙasa ba tare da la’akari da bambancin ƙabila, addini, ko ra’ayin siyasa ba.
