Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan manyan kamfanonin mai, yana zarginsu da kin rage farashin fetur duk da raguwar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya.
Trump ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, inda ya ce kamfanonin mai na ci gaba da sayar da fetur da tsada duk da cewa farashin ɗanyen man da suke saya ya ragu sosai.
Farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabo bayan Iran ta toshe hanyar safarar mai ta mashigar ruwa ta Strait of Hormuz, a matsayin martani ga hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai mata a watan Fabrairu.
Batun farashin fetur na da matuƙar tasiri a siyasar Amurka, kasancewar yawancin al’ummar ƙasar na amfani da motoci masu amfani da makamashin fetur wajen zirga-zirgarsu ta yau da kullum.
Trump na fuskantar suka daga wasu ‘yan ƙasa da masu sharhi kan yadda rikicin Gabas ta Tsakiya ya shafi tattalin arziki da kuma ƙarin kuɗin da jama’a ke kashewa wajen sayen fetur, musamman yayin da zaɓen ‘yan majalisar dokokin ƙasar ke ƙaratowa.
Duk da cewa shugaban ya sha alwashin cewa farashin fetur zai ragu sosai bayan ƙarshen rikicin, masana tattalin arziki na ganin cewa farashin mai ba zai koma yadda yake kafin rikicin ba sai bayan wasu watanni.
A halin yanzu, Tehran da Washington sun cimma yarjejeniya ta farko da ta bai wa tankokin dakon mai damar komawa amfani da mashigar Hormuz, duk da cewa har yanzu akwai sabani kan shirin makamashin nukiliyar Iran.
Bisa ga bayanan ƙungiyar masu motoci ta AAA, matsakaicin farashin galan ɗaya na fetur (kimanin lita 3.8) ya kai dala 3.93 a ranar Talata. Ko da yake farashin ya ɗan sauka bayan sanarwar yarjejeniyar farko tsakanin bangarorin biyu, har yanzu yana sama da matakin da yake kafin barkewar rikicin.
Masu sukar Trump na zarginsa da kashe biliyoyin dalolin masu biyan haraji wajen yaƙin Gabas ta Tsakiya, yayin da farashin mai da hauhawar farashi ke ci gaba da ƙaruwa a cikin Amurka kamar yadda kafar yada labaraita AFP ta tattaro.
