DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeKasuwanciTakardun kudi fiye da Naira tiriliyan 5 ne ke yawo a hannun...

Takardun kudi fiye da Naira tiriliyan 5 ne ke yawo a hannun jama’a a Nijeriya – CBN

Duk da shekaru da aka kwashe na aiwatar da manufar rage amfani da yawan takardun kuɗi a hannu (Cashless Policy) da kuma ƙarfafa amfani da hanyoyin biyan kuɗi ta yanar gizo, alkaluman da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fitar sun nuna cewa har yanzu ‘yan Najeriya na riƙe da kuɗaɗe masu yawa a wajen tsarin bankuna.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito sabbin bayanan CBN sun nuna cewa adadin kuɗin da ke wajen bankuna ya kai Naira tiriliyan 5.19 a watan Mayun 2026, daga Naira tiriliyan 5.08 da aka samu a watan Afrilu na shekarar nan.

Wannan na nufin an samu ƙarin Naira biliyan 109.34 cikin wata guda, wanda ya kai kaso 2.15 cikin ɗari.

A cewar CBN, manufar rage amfani da kuɗi a hannu da aka ƙaddamar da domin ƙarfafa biyan kuɗi ta yanar gizo, shine faɗaɗa harkokin hada-hadar kuɗi, rage kuɗaɗen sarrafa takardun kuɗi da kuma ƙara gaskiya a tsarin kuɗi na ƙasa.

Sai dai duk da bunƙasar hanyoyin amfani da kuɗi ta banki, karuwar na’urorin POS da kuma ayyukan wakilan bankuna a kasuwanni, har yanzu kuɗi a hannu na ci gaba da kasancewa hanyar mu’amala da mafi yawan ‘yan Najeriya ke amfani da ita, musamman masu gudanar da sana’o’i a ɓangaren tattalin arziki na yau da kullum.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata