DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, May 19, 2026
HomeKetareTrump ya dakatar da kai wa Iran hari a dalilin kasashen Gulf

Trump ya dakatar da kai wa Iran hari a dalilin kasashen Gulf

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ya dakatar da shirin kai wani sabon hari kan kasar Iran bayan samun rokon shugabannin kasashen Larabawa na yankin Gulf domin bai wa tattaunawar zaman lafiya dama.

Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa Trump ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, inda ya ce ya na shirin kai harin a ranar Talata kafin daga bisani ya sauya matsaya.

A cewarsa, shugabannin kasashen Qatar, Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa ne suka bukace shi ya dakatar da shirin harin saboda ana hango haske a tattaunawar neman sulhu tsakanin bangarorin da ke rikici.

Trump ya ce duk da dakatar da harin, ya umurci rundunar sojin Amurka ta kasance cikin shirin ko-ta-kwana domin kai gagarumin farmaki idan har ba a cimma yarjejeniyar da Amurka za ta amince da ita ba.

Da yake magana a wani taro a Fadar White House, shugaban na Amurka ya ce akwai alamun samun nasara a tattaunawar ba tare da sake kai hare-hare ba.

Ya kara da cewa kasashen Larabawan Gulf sun tabbatar masa cewa ana gab da cimma yarjejeniyar da za ta hana Iran mallakar makamin nukiliya, duk da cewa Tehran na ci gaba da musanta zargin ta na kokarin kera irin wadannan makamai.

A bangaren Iran kuwa, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar, Esmaeil Baqaei, ya tabbatar da cewa ana ci gaba da musayar sakonni tsakanin Tehran da Washington ta hannun kasar Pakistan da ke shiga tsakani.

Rahotanni sun nuna cewa Iran na neman a sako wasu kadarorinta da ke kasashen waje, da kuma dage mata takunkuman tattalin arziki da aka kakaba mata tun shekaru masu yawa da suka gabata.

Haka kuma shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana cewa tattaunawa da Amurka ba yana nufin mika wuya ba ne, tare da jaddada cewa kasarsa za ta kare martabarta da hakkokinta.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata