DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, May 19, 2026
HomeKetareTogo ta cire bukatar biza ga matafiya ‘yan Afirka

Togo ta cire bukatar biza ga matafiya ‘yan Afirka

Gwamnatin ƙasar Togo ta sanar da cire buƙatar biza ga dukkan ‘yan ƙasashen Afirka da ke shiga ƙasar domin zama na wani ɗan lokaci.

An bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Tsaro ta Togo ta fitar a shafinta na X a ranar Talata, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A cewar sanarwar, duk wani ɗan Afirka mai riƙe da ingantaccen fasfo na ƙasarsa zai iya shiga Togo ba tare da neman biza ba domin zama har na tsawon kwanaki 30.

Gwamnatin Togo ta ce wannan mataki wani ɓangare ne na ƙoƙarin ƙara ƙarfafa haɗin kan ƙasashen Afirka tare da sauƙaƙa zirga-zirga tsakanin al’ummomin nahiyar.

Sanarwar ta bayyana cewa shugaban majalisar ƙasar ya sake jaddada aniyarsa ta mayar da Togo cibiyar hulɗa da jama’a , haɗin kai da damar kasuwanci a tsakiyar nahiyar Afirka.

Sai dai duk da cire bukatar biza, gwamnatin ta ce matafiya za su ci gaba da cike takardar bayanan tafiya a shafukan gwamnati kafin akalla sa’o’i 24 da isa ƙasar domin samun takardar izinin shiga.

Ma’aikatar tsaron ta ce sabon tsarin zai taimaka wajen ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen Afirka tare da bunƙasa harkokin kasuwanci da yawon buɗe ido.

Matakin ya sanya Togo cikin jerin ƙasashen Afirka da suka sassauta dokokin shiga ƙasarsu ga sauran ‘yan Afirka domin ƙarfafa haɗin kan yankin.

Rahotanni sun nuna cewa ƙasar Rwanda ma ta ɗauki irin wannan mataki a baya, inda ta bai wa ‘yan Afirka damar shiga ƙasar ba tare da biza ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata