Jam’iyyar ADC a jihar Kebbi, arewa maso yammacin Nijeriya ta bayyana cikakken goyon bayanta ga tsohon Babban Lauyan larayya kuma Ministan Shari’a na Nijeriya, Abubakar Malami, ta re da cewa shari’ar da ake yi masa tana da alaƙa da siyasa, kuma ba za ta kawo cikas ga shirye-shiryenta na babban zaɓen 2027 ba.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa jam’iyyar ta fadi hakan ne a sanarwar bayan taron shugabanninta na jihar da aka gudanar a Sakkwato, inda ta jaddada aniyarta ta ci gaba da mayar da hankali kan burinta na kayar da jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027.
Sanarwar, wacce Shugaban ADC na jihar Kebbi, Sufiyanu Bala da Shugaban Majalisar dattawan jam’iyyar, Shehu Aliyu Sambawa suka sanya wa hannu, ta zargi gwamnatin tarayya ƙarƙashin APC da amfani da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma wasu sassan ɓangaren shari’a wajen matsa wa ‘yan adawa lamba gabanin zaɓen 2027.
Jam’iyyar ta ce ba ta adawa da gudanar da sahihin bincike ko gurfanar da duk wanda ake zargi da aikata laifi bisa doka, amma ta yi Allah wadai da abin da ta kira amfani da hanyoyin danniya domin raunana ‘yan adawa da kuma dakile ra’ayoyin masu adawa da gwamnati.
A cewar ADCin ta Kebbi, duk wani yunƙurin takura wa shugabanninta ba zai sa ta kauce daga manufarta ta ganin an kayar da gwamnatin APC a zaɓen 2027 ba.
Jam’iyyar ta kuma zargi APC da ƙoƙarin sanya siyasar adawa ta zama mai wahala ta hanyar amfani da cibiyoyin gwamnati da hukumomin tsaro.
Ta ce manufofin tattalin arzikin gwamnatin tarayya da kuma yadda ake amfani da wasu cibiyoyin gwamnati sun rage amincewar jama’a da APC.
Dangane da binciken da ake yi wa Malami da kuma umarnin kotu na ƙwace kadarori 48 da ake alaƙanta da shi, ADC ta yi zargin cewa koken da aka shigar, binciken, kamawa, tsarewa da kuma gurfanar da tsohon ministan an tsara su ne domin cimma wata manufa ta siyasa.
Jam’iyyar ta kuma yi ikirarin cewa jami’an tsaro sun binciki kadarorin Malami ba tare da kasancewarsa a wurin ba, tare da ƙara darajar kadarorin da ake dangantawa da shi da iyalansa domin bata masa suna a idon jama’a.
