Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta dakatar da Kakakin Majalisar Ƙaramar Hukumar Auyo, Haruna Maigari, bisa zargin aikata ayyukan da suka saɓa wa manufofin jam’iyyar APC, lamarin da ake zargin na barazana ga haɗin kan jam’iyyar a matakin ƙasa da ƙasa.
Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, majalisar ta ɗauki matakin ne a zaman da ta yi ranar Talata a Dutse bayan la’akari da kudirin da Jagoran Majalisa, Lawan Dansure, ya gabatar yana neman a hukunta Maigari kan abin da ya kira ayyukan da ke kawo cikas ga haɗin kan jam’iyyar.
Dakatarwar na zuwa ne yayin da APC a Jigawa ke ci gaba da fuskantar rikice-rikicen da suka biyo bayan zaɓen fidda gwani, inda aka dakatar da wasu masu ba gwamnati shawara da mataimaka a matakai daban-daban bisa irin wannan zargi.
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, Haruna Dangyatin, ya sanar da dakatarwar nan take tare da kafa kwamitin bincike domin gano gaskiyar lamarin da kuma gabatar da rahotonsa cikin makonni biyu.
Majalisar ta kuma umarci Haruna Maigari, wanda ke wakiltar mazabar Auyo a majalisar ƙaramar hukumar, da ya miƙa duk wasu takardun ofis da ke hannunsa ga mataimakin kakakin majalisar domin tabbatar da ci gaba da gudanar da ayyukan majalisar ba tare da tangarda ba.
