Wasu ƴan bindiga sun sace Olaide Busayo Adegoke John-Paul, ƙanwar tsohon Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, tare da ƴaƴanta tagwaye biyu a birnin Ibadan na jihar Oyo.
Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, lamarin ya faru ne da safiyar Laraba a yankin Challenge da ke ƙaramar hukumar Ibadan South West yayin da Olaide ke kan hanyarta ta kai ƴaƴanta makaranta.
Mai taimaka wa Adelabu kan harkokin yaɗa labarai, Femi Awogboro, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa. Ya ce maharan sun yi awon gaba da Olaide mai shekara 43 tare da tagwayenta Peter da Paul masu shekara 12.
Sanarwar ta ce jami’an tsaro sun fara bincike da kuma ƙoƙarin ceto waɗanda aka sace bayan an kai musu rahoton lamarin. Iyalan Adelabu sun bayyana damuwarsu kan abin da ya faru, amma sun nuna ƙwarin gwiwa cewa jami’an tsaro za su kubutar da su cikin koshin lafiya.
Iyalan sun kuma yi kira ga jama’a da su guji yaɗa jita-jita ko bayanan da ba a tabbatar da su ba, tare da buƙatar duk wanda ke da wani bayani da zai taimaka wajen bincike ya sanar da hukumomin tsaro.
