DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeLabaraiWajibi ne a yi cikakken bincike kan kisan Ɗan Shagamu - Obi

Wajibi ne a yi cikakken bincike kan kisan Ɗan Shagamu – Obi

Tsohon gwamnan jihar Anambra kuma dan takarar shugaban Nijeriya na jam’iyyar NDC a zaben 2027, Peter Obi, ya bukaci a gudanar da cikakken bincike kan kisan wani mai sharhi kan al’amuran siyasa a kafafen sada zumunta, Ibrahim Khalil Dan Shagamu, mazaunin Kano.

Obi ya yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Juma’a, inda ya yi Allah-wadai da kisan tare da bukatar gwamnatin jihar Kano da hukumomin tsaro su tabbatar da hukunta wadanda suka aikata laifin, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

An kashe Dan Shagamu ne a gidansa da ke unguwar Gaida da ke karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano, a daren ranar Litinin.

Rundunar ’yansandan Kano ta ce ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a lamarin.

A cewar ’yansandan, lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:30 na dare, bayan kwamandan kungiyar sa-kai ta Gaida ya kai rahoton cewa wasu ’yan daba da ba a san ko su wanene ba sun kutsa gidan Dan Shagamu da karfi tare da kai masa hari da makamai masu kaifi.

Jami’an ’yansanda daga sashen Kumbotso sun garzaya wurin, inda suka kai Dan Shagamu asibitin kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano, sai dai an tabbatar da rasuwarsa.

Rundunar ta ce wadanda ake zargin suna hannunta kuma ana yi musu tambayoyi, yayin da ake gudanar da binciken kwakwaf domin gano hakikanin yadda lamarin ya faru da kuma dalilin kai harin.

Da yake mayar da martani kan kisan, Peter Obi ya ce sabani ko suka bai kamata su zama dalilin haddasa da tashin hankali ba.

Obi ya bukaci gwamnatin jihar Kano da hukumomin tsaron da abin ya shafa su gudanar da “cikakken bincike cikin gaskiya kuma ba tare da nuna bangaranci ba”.

Ya kuma bukaci a gurfanar da duk wadanda ke da hannu a kisan a gaban kotu, yana mai jaddada cewa kundin tsarin mulkin Nijeriya ya bayar da ’yancin fadin albarkacin baki.

Peter Obi ya jajantawa iyalan Dan Shagamu, abokansa da mabiyansa, tare da addu’ar Allah ya ji kan sa ya kuma yi masa rahama.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata