DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, October 3, 2026
HomeLabaraiYan sandan Kano sun jaddada cewa dokar hana hawan doki na nan...

Yan sandan Kano sun jaddada cewa dokar hana hawan doki na nan daram

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta sake jaddada dokar hana gudanar da hawa doki a wuraren taruwar jama’a, tare da gargadin masu shirya irin waɗannan bukukuwa da su bi umarnin hukumomi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai bayani a hedikwatar rundunar da ke Bompai, Kano.

Bakori ya ce gwamnatin jihar ta sanya dokar ne bayan tuntubar hukumomin tsaro, domin kare zaman lafiya da tabbatar da doka da oda a jihar.

Ya bayyana damuwa kan rahotannin karya dokar, yana mai cewa matsalolin tsaron da suka sanya aka takaita gudanar da ayyukan suna nan daram.

Kwamishinan ya ce taron hadin gwiwar hukumomin tsaro ya yanke shawarar cewa duk wanda ke son shirya durbar ko wasan hawa doki a bainar jama’a, dole ne ya gabatar da rubutacciyar takarda ga rundunar ’yan sanda aƙalla sa’o’i 72 kafin gudanar da taron.

Ya ce hakan zai bai wa ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro damar tantance barazanar tsaro da kuma yin shirye-shiryen da suka dace domin kare mahalarta taron da sauran jama’a.

Bakori ya bukaci al’umma, sarakunan gargajiya da masu shirya bukukuwa da su bi umarnin, tare da ba hukumomin tsaro hadin kai wajen tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyi a fadin jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata