DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeSiyasa‘Yan adawa ba za su iya kayar da Tinubu a zaben 2027...

‘Yan adawa ba za su iya kayar da Tinubu a zaben 2027 ba – Fayose

Tsohon Gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya bayyana cewa shugaban Nijeriya, Bola Tinubu, ne ke kan gaba wajen damar lashe zaben shugaban kasa na 2027, yana mai cewa rarrabuwar kawunan jam’iyyun adawa ta raunana karfinsu na kalubalantar sa.

Da yake magana a wata hira da ya yi gidan talabijin na Channels a ranar Litinin, Fayose ya ce jam’iyyun adawa sun rage wa kansu damar samun nasara saboda gaza hada kai a karkashin tsari guda kafin zaben.

Ya kuma yi watsi da ra’ayoyin da ke cewa Tinubu na fuskantar babbar barazana a zabe duk da matsalolin rashin tsaro, tsadar rayuwa da kuma kalubalen tattalin arziki da ake fuskanta a fadin kasar.

A cewarsa, da jam’iyyun adawa sun samu nasarar kafa kawance mai karfi tare da tsayawa a jam’iyya guda, da Tinubu zai fuskanci gagarumar hamayya.

Fayose ya kuma ce yawaitar jam’iyyun siyasa da masu neman takarar shugaban kasa ya kara rage yiwuwar nasara ga bangaren adawa.

Ya kwatanta lamarin da yadda zaben shugaban kasa na 2023 ya gudana, yana mai cewa rarrabuwar kawunan adawa na iya sake zama wani abin da zai yi wa Tinubu aiki a zaben 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata