Shugaban jam’iyyar APC Nentawe Yilwatda, ya ce jam’iyyar na da cikakkun hanyoyin sasanta rikice-rikicen da suka taso bayan zaɓukan fidda gwani da aka gudanar a jihohi daban-daban na ƙasar nan.
Yilwatda ya bayyana hakan ne bayan wata ganawa da ya yi da Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, a birnin Legas ranar Laraba.
Jaridar Daily Trust ta rawaito shugaban jam’iyyar na cewa zaɓukan fidda gwanin da APC ta gudanar sun kasance daga cikin masu zafi a tarihin siyasar Nijeriya saboda yadda jam’iyyar ke samun karɓuwa a faɗin ƙasar.
Ya yabawa shugaban ƙasa da mambobin jam’iyyar bisa goyon bayan da suka bayar yayin gudanar da zaɓukan, yana mai cewa an gudanar da mafi yawan zaɓukan cikin tsari da kwanciyar hankali ba tare da manyan rikice-rikice ba.
A cewarsa, duk da cewa ana samun ƙorafe-ƙorafe a duk lokacin zaɓe, amma tsarin zaɓukan fidda gwani na APC ya kasance cikin nagarta idan aka kwatanta da yadda ake gudanar da irin waɗannan zaɓuka a baya.
Ya ce zaɓukan sun kasance cikin tsari sosai kuma an samu ƙarancin rikice-rikice.
A shugaban jam’iyyar korafi abu ne da aka saba gani a lokacin zaɓe, amma wannan karon an gudanar da shi cikin kwanciyar hankali.
Shugaban ya kuma bayyana cewa APC na da kwamitocin sasanta rikice-rikice da aka kafa domin duba koke-koken da suka taso bayan zaɓukan fidda gwani.
A cewarsa, akwai kwamitin sasanta rikice-rikicen jam’iyya da kuma kwamitin sasanta rikice-rikicen Shugabanci da za su tabbatar da warware matsalolin cikin gida domin haɗa kan jam’iyyar kafin babban zaɓen 2027.
Yilwatda ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu ya nuna gamsuwa da yadda jam’iyyar ta tsara harkokin gudanar da zaɓukan fidda gwani a faɗin ƙasar nan, musamman yadda aka samu ƙarancin tashin hankali da rikice-rikice a mafi yawan jihohi.
