Kabiru Adamu Abdullahi, wani tsohon jigo a tafiyar Kwankwasiyya kuma na hannun daman mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya fice daga jam’iyyar tare da komawa APC.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Abdullahi, wanda ya shafe shekaru 29 yana tare da Kwankwaso, ya taɓa rantsuwa da Alƙur’ani domin tabbatar da amincinsa ga jagoran Kwankwasiyya bayan rabuwar da aka samu tsakaninsa da Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Abdullahi ya sanar da ficewarsa daga NDC ne cikin wata wasiƙar murabus da ya aika wa shugaban jam’iyyar na mazabar Kofar Ruwa da ke ƙaramar hukumar Dala a jihar Kano.
Ya ce abin da ya sa ya ɗauki matakin shi ne takaicinsa kan abin da ya bayyana da cewa “alkawuran da ba a cika ba” a cikin jam’iyyar NDC.
Ya bayyana cewa yanzu zai mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin sake zaɓensa a ƙarƙashin jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
Abdullahi ya ce: “Na shafe shekaru 29 ina tare da Kwankwaso, amma abin da na samu shi ne alkawuran da ba a cika ba, zan je inda za a fi girmama ni.”
A cikin wasiƙar murabus ɗin, ɗan siyasar ya gode wa jam’iyyar NDC bisa damar da ta ba shi ta yi mata hidima, kafin ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar nan take.
Ficewar Abdullahi na zuwa ne yayin da ake samun sauye-sauyen siyasa da sauya sheka tsakanin manyan ’yan siyasa da magoya bayan jam’iyyun siyasa gabanin babban zaɓen 2027.
