Aƙalla mutane uku ne aka hallaka, yayin da wasu mutum biyu suka jikkata sakamakon harin da wasu ’yan bindiga suka kai a wurin aikin gina babbar hanyar Sokoto zuwa Badagry, a ƙaramar hukumar Maiyama ta Jihar Kebbi.
Wadanda aka kashe sun haɗa da jami’an tsaro biyu da wani ɗan ƙasar waje da ke aiki a aikin gina hanyar, yayin da fararen hula biyu suka samu raunukan a dalilin harbin bindiga.
Kakakin Rundunar ƴan Sandan Jihar Kebbi, Sufeto Bashir Usman, ya ce lamarin ya faru ne a wani wurin aikin gina hanya da ke ƙauyen Gubba, a yankin Andarai na ƙaramar hukumar Maiyama.
Usman ya ce wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan ta’addan Lakurawa ne, waɗanda suka shigo daga yankin Kebbe na makwabciyar Jihar Sokoto, sun kai hari wurin aikin, inda suka kashe jami’an tsaro biyu da wani ɗan ƙasar waje.
Ya ce harin ya kuma jikkata fararen hula biyu, waɗanda aka garzaya da su asibiti domin samun kulawar likitoci, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
Kakakin ’yan sandan ya ƙara da cewa a wannan rana, jami’an tsaro sun kuma dakile wani harin da waɗanda ake zargin ’yan ta’addan ne suka kai a yankin Birnin Malam.
Ya ce jami’an tsaro na haɗin gwiwa sun mayar da martani ga hare-haren, inda aka tura rundunonin musamman domin ƙarfafa tsaro da hana sake kai wasu hare-hare.
PPRO ɗin ya kuma bayyana cewa dakarun soji sun kashe da dama daga cikin maharan, yayin da aka kwato babura da dama.
Bayan harin, an dakatar da ayyukan gine-ginen hanyar a wurin da lamarin ya faru, yayin da hukumomin tsaro suka ƙara sa ido tare da tura ƙarin jami’ai zuwa yankin.
PPRO ɗin ya tabbatar wa ma’aikatan aikin cewa gwamnati ta himmatu wajen tabbatar da tsaron lafiyarsu, inda ya buƙace su da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da jajircewa yayin da hukumomin tsaro ke ƙoƙarin kare rayukansu da dukiyoyinsu.
A baya-bayan nan, Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya ziyarci Jandutsi da wasu ƙauyukan da ke makwabtaka da ƙauyen Gubba domin jajanta wa mazauna yankin kan hare-haren ’yan bindiga da aka kai a yankin.
Gwamnan ya kuma sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta ƙara ƙarfafa tsaro da kare al’ummomin da hare-haren suka shafa.
