Babban daraktan asusun horar da ma’aikata na ƙasa (ITF), Dakta Afiz Ogun, ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin da Shugaba Bola Tinubu ke aiwatarwa suna samun nasara, yana mai cewa ƴan Nijeriya za su fi farin ciki idan aka sake zaɓen shugaban ƙasar a wa’adi na biyu.
Ogun ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a Jos, yayin bikin cika shekaru 55 da kafa ITF, da kuma bikin cika shekaru uku da ya yi yana jagorantar hukumar, kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.
Daraktan ya bayyana cewa kafin ya fara karanta jawabin da ya shirya, ya yanke shawarar yin kamfen ga Shugaba Tinubu ne bayan ya lura da yadda mahalarta taron da baƙi suke kallon sauye-sauyen da ake samu a ƙasar.
Ya ce: “Na tabbata masu horarwa da ke nan sun fahimci abin da nake magana a kai. Yayin da abokin aikina yake magana kan ci gaban da ake samu a fannin man fetur da iskar gas, ni kuma ina nazarin yanayin da ke cikin wannan ɗaki.
Shugaban ITF ɗin ya ce Shugaba Tinubu ya naɗa shi a shekarar 2023 duk da cewa a baya ba su taɓa sanin juna ba, yana mai cewa hakan na nuna yadda shugaban ke neman ƙwararrun mutane domin su yi masa aiki.
Ya ce: “Na bar Nijeriya a shekarar 2004, ban dawo ba sai a shekarar 2023 lokacin da wani mutum da bai san ni ba ya naɗa ni. Abin da yake nema kawai shi ne ƙwararrun mutane, kamar yadda ya yi lokacin da yake Gwamnan Legas.
Yace ku legas a yau. A duk faɗin Afirka, ƙasashe uku ne kawai suka fi Jihar Legas arziki. Ba haka lamarin yake ba kafin ya zo. Ya kafa harsashin ci gaban jihar, ya kula da ita tare da kare ta kamar yadda kaza ke kare ’ya’yanta, har ma lokacin da wasu shugabannin ƙasa suka yi adawa da shi.
Ya ce: “Wani lokaci idan shugaba nagari ya yi abin da ya yi kama da baƙon abu, mutane kan yi Allah-wadai da shi ba tare da zurfafa tunani ba.”
Ogun ya ce manyan dalilai biyu da suka sa wasu ƴan Nijeriya ke ƙin Shugaba Tinubu a yanzu — cire tallafin man fetur da farashin musayar kuɗi — a zahiri matakan ne da suke da amfani ga ƙasar.
