Ma’aikatan da ke karkashin ƙungiyar Support Staff Union ta Kamfanin Matatar Mai na Fatakwal (PHRC), sun yi barazanar dakatar da ayyukan matatar saboda rashin biyansu albashi na tsawon watanni bakwai.
Ma’aikatan sun kuma zargi mahukuntan kamfanin da kin aiwatar da sabon tsarin albashin da aka amince da shi, inda suka ba hukumomin kamfanin wa’adin sa’o’i 48 da su magance bukatunsu ko kuma su fuskanci dakatar da ayyukan matatar.
A ranar Laraba ne ma’aikatan suka tare kofar shiga matatar da ke Jihar Rivers, inda suka fito da allunan rubuce-rubuce tare da kafa tantuna a bakin kofar matatar.
Zanga-zangar ta haifar da tsaiko na wani lokaci ga ayyukan da ake gudanarwa a cikin matatar, kamar yadda Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito
Wasu daga cikin rubuce-rubucen da ke jikin allunan sun hada da: “Ba za mu sake yarda da alkawuran banza ba, Janairu 2027 ya yi nisa wajen aiwatar da sabon tsarin albashi,” “Dole ne Kodinetan Matatar ya sauka,” da kuma “Babban Daraktan NNPCL ya amince da sabon tsarin a ranar 1 ga Oktoba, amma Kodinetan Matatar ya ki amincewa da shi, Ma’aikatan tallafi na bukatar Kodinetan ya sauka.”
Ma’aikatan sun yi zargin cewa Bayo Ojulari, Babban Daraktan Gudanarwa na Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL), ya amince da sabon tsarin albashi da kunshin alawus-alawus ga ma’aikatan.
Sai dai sun ce Kodinetan Matatar ya ki aiwatar da wannan umarni.
Ma’aikatan sun bayyana zanga-zangar a matsayin ta lumana, wadda suka ce sun gudanar ne domin nuna adawa da abin da suka kira rashin adalci da kuma nuna musu wariya.
