Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya bukaci jiga-jigan siyasar Arewa da su mayar da hankali wajen samar da tsari na bai ɗaya domin magance matsalolin yankin, maimakon mayar da hankali kacokan kan fafutukar neman ikon siyasa a matakin tarayya.
Uba Sani ya bayyana rashin zuwa makaranta da yara, ƙarancin ilimin koyon sana’o’i da kuma gazawar tsarin samar da ingantaccen kiwon lafiya a matsayin wasu daga cikin manyan matsalolin da ke addabar yankin Arewa, kamar yadda Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, lokacin da shugabannin gidauniyar Sir Ahmadu Bello Memorial Foundation suka kai masa ziyarar ban-girma a zauren majalisar zartaswa ta Gidan Gwamnatin Jihar Kaduna.
Ya yaba wa gidauniyar bisa yadda take jawo hankalin shugabannin siyasar Arewa kan muhimmancin bai wa bunƙasa jarin ɗan Adam fifiko, yana mai cewa yankin ba shi da tsari na bai ɗaya da zai jagoranci yadda za a magance matsalolinsa.
Uba Sani ya ce taron koli na Sir Ahmadu Bello Memorial Foundation da ke tafe, mai taken “Kyakkyawan Shugabanci, Masana’antu da Ƙirƙire-Ƙirƙire, da kuma Ci Gaba Mai ɗorewa”, ya zo a kan lokaci.
Ya ce, “Na yi farin ciki da ganin Sir Ahmadu Bello Memorial Foundation na jagorantar wannan yunƙuri, domin muna buƙatar zama tare, mu duba matsalolinmu, sannan mu magance su ta hanya mai faɗi da ta shafi dukkan ɓangarori.”
Gwamnan ya kuma nuna damuwa kan yawan mace-macen mata masu juna biyu da yara a Arewacin Nijeriya, da kuma yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, tare da ƙarancin ilimin koyon sana’o’i a yankin.
Ya ce gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen ƙarfafa cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko domin biyan buƙatun marasa galihu da mazauna yankunan karkara, tare da inganta ayyukan kiwon lafiya na matakin sakandare.
Ya ce, “A wurinmu, kiwon lafiya a Kaduna haƙƙi ne na kowa, musamman marasa galihu da masu rauni a cikin al’ummarmu.”
Da yake ambaton alkaluman UNICEF, Uba Sani ya ce Najeriya na da kusan yara miliyan 18 da ba sa zuwa makaranta, inda kashi 70 cikin 100 daga cikinsu suke Arewacin Najeriya.
Ya ce sama da yara 500,000 ne ke yawo a titunan Jihar Kaduna lokacin da ya kama mulki, inda ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta mayar da kusan 360,000 daga cikinsu makaranta.
A cewarsa, tsarin taswirar gidaje da jihar ta yi amfani da shi wajen gano yaran da ba sa zuwa makaranta, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta ɗauke shi a matsayin abin koyi wajen magance matsalar a faɗin ƙasar.
Dangane da ilimin koyon sana’o’i, Sani ya ce Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya rubuta masa wasiƙa kimanin watanni uku da suka gabata, inda ya nemi Jihar Kaduna ta ba Gwamnatin Nijeriya damar amfani da tsarin da jihar ta samar.
