DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeLabaraiƊan Gwamnan Bauchi ya roƙi mahaifinsa ya biya ma’aikatan da suka yi...

Ɗan Gwamnan Bauchi ya roƙi mahaifinsa ya biya ma’aikatan da suka yi ritaya haƙƙoƙinsu

Ɗan Gwamnan jihar Bauchi, Shamsuddeen Bala Mohammed, ya buƙaci mahaifinsa, Gwamna Bala Mohammed, da ya gaggauta biyan kuɗaɗen garatutin ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya tare da ƙaddamar da shirye-shiryen ƙarfafa matasa domin rage matsin tattalin arzikin da ake fama da shi a jihar.

Shamsuddeen ya bayyana hakan ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A cikin saƙon, ya yabawa gwamnatin mahaifinsa kan manyan ayyukan gine-ginen tituna, makarantu da asibitoci da ta aiwatar cikin shekaru bakwai da suka gabata, yana mai cewa waɗannan ayyuka za su kasance abin alfahari ga al’ummomin jihar a nan gaba.

Sai dai ya nuna cewa duk da irin ci gaban da aka samu a fannin ababen more rayuwa, har yanzu jama’a musamman matasa na fama da matsanancin ƙalubalen tattalin arziki.

A cewarsa, mutane da dama na ganin cewa gina tituna da sauran ayyukan raya ƙasa kaɗai ba za su magance matsalolin rayuwar yau da kullum ba, musamman yadda iyalai ke ci gaba da jiran a biya ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya haƙƙoƙinsu.

Shamsuddeen ya ce jinkirin biyan waɗannan kuɗaɗe ya ƙara jefa iyalai cikin mawuyacin hali, yayin da rashin ayyukan yi da damar samun kuɗaɗen shiga ke ƙara haifar da rashin jin daɗi a tsakanin matasa.

Ya yi gargadin cewa akwai alamun samun ƙorafi daga matasa, yana mai cewa ba tallafi kawai suke nema ba, illa suna son a ba su damar shiga cikin tattalin arzikin jiharsu.

Domin magance matsalar, ya ba da shawarar gwamnatin jihar ta karkata hankali wajen bunƙasa matasa ta hanyar samar da tallafin fara kasuwanci ga matasa, ba da jarin tallafi ga ƙananan ’yan kasuwa da kuma tilasta wa kamfanonin da ke gudanar da ayyukan gwamnati ɗaukar matasan Bauchi aiki.

Ya ƙara da cewa ya kamata gwamnati ta rungumi manufofin da za su mayar da hankali kan zuba jari a rayuwar jama’a, ba wai gina ababen more rayuwa kaɗai ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata