DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeKetare'Mutum 1,430 sun mutu a girgizar ƙasa a Venezuela'

‘Mutum 1,430 sun mutu a girgizar ƙasa a Venezuela’

Gwamnatin ƙasar Venezuela ta ce mutum akalla 1,430 ne suka mutu, yayin da ake ci gaba da neman sama da mutum 51,000 bayan girgizar ƙasa biyu masu ƙarfi da suka afku ranar Laraba a yankin La Guaira da ke gabar tekun ƙasar.

Kamar yadda kafar Al Jazeera da AP suka ruwaito, girgizar ƙasar mai ƙarfin maki 7.2 da 7.5 ta haddasa rushewar gine-gine da lalacewar manyan ababen more rayuwa, lamarin da ya sa jami’an ceto ke ci gaba da neman waɗanda suka maƙale a ƙarƙashin baraguzai.

Jami’an ceto da mazauna yankunan da abin ya shafa na ta amfani da hannu wajen tono mutane daga ƙarƙashin gine-ginen da suka rushe, yayin da hukumomi suka ce sa’o’i 72 na farko da ake sa ran samun waɗanda ke raye na gab da ƙarewa.

Yadda girgizar ƙasar ta afku

Girgizar ƙasar ta afku ne cikin tazarar lokaci kaɗan tsakaninta, abin da masana suka ce ya ƙara tsananta ɓarnar da aka samu. Yankin La Guaira ne ya fi fuskantar matsala, inda gwamnati ta fara takaita shiga yankin saboda cunkoson ababen hawa da ya hana ayyukan ceto gudana yadda ya kamata.

Shugabar riƙon ƙasar Venezuela, Delcy Rodriguez, ta ce gwamnati ta tura jami’an tsaro da kayan agaji domin taimaka wa waɗanda bala’in ya shafa.

Ta ce, “Muna cikin muhimman sa’o’i na ceton mutanen da ake sa ran suna raye.”

Jama’a na zargin rashin isassun jami’an ceto

Sai dai rahotanni daga yankunan da abin ya shafa sun nuna cewa mutane da dama na korafin rashin isassun jami’an ceto daga gwamnati.

Wasu mazauna yankin sun ce su ne suka fi gudanar da aikin neman waɗanda suka maƙale a ƙarƙashin gine-gine da hannayensu saboda ƙarancin kayan aiki da jami’ai.

Shugaban Majalisar Dokokin Venezuela, Jorge Rodriguez, ya ce gwamnati ba za ta ɓoye girman bala’in da ya afku ba.

“Duk mutumin da aka ceto babbar nasara ce,” in ji shi.

Ƙasashen duniya sun fara kai ɗauki

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ɓarnar da girgizar ƙasar ta haddasa na iya kaiwa tsakanin dala biliyan 4.7 zuwa biliyan 8.7.

Hukumar IOM ta ce mutum kusan miliyan 6.7 na iya fuskantar matsalar matsuguni da sauran matsaloli sakamakon bala’in.

Haka kuma hukumomin Venezuela sun ce jami’an ceto 1,600 daga ƙasashen waje sun isa ƙasar domin taimakawa aikin ceto.

Matsalar sadarwa da neman ‘yan uwa

Wakiliyar Al Jazeera daga Caracas, Noris Soto, ta ce mutane da dama sun kasa gano inda ‘yan uwansu suke saboda matsalar katsewar layukan waya da intanet musamman a jihar La Guaira.

Ta ce wasu mazauna yankin na korafin cewa ba su san inda ake kai waɗanda aka ceto ko gawarwakin da aka gano ba.

Kazalika masu aikin ceto sun bayyana cewa damar samun waɗanda ke raye na ƙara raguwa yayin da ake ci gaba da girgizar ƙasa bayan afkuwar ta farko.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata