DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeLabarai‘Ba za mu ɗauki tubabbun ƴan ta’adda aikin ƴan sanda ba’

‘Ba za mu ɗauki tubabbun ƴan ta’adda aikin ƴan sanda ba’

Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya ta ce ba za ta ɗauki tubabbun ‘yan ta’adda ko masu laifi aiki cikin rundunar ba, tare da gargadin shugabannin al’umma da jami’an tsaro su guji ba su takardun shaidar kyawawan ɗabi’u domin shiga aikin hukumomin tsaro.

Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda mai kula da shiyyar Arewa ta Tsakiya, DIG Isyaku Mohammed, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da jami’an rundunar ‘yan sanda da masu ruwa da tsaki a Ilorin, Jihar Kwara.

Taron ya haɗa da sarakunan gargajiya, shugabannin addini, ƙungiyoyin sufuri da sauran shugabannin al’umma, inda DIG ɗin ya buƙace su da kada su riƙa sanya hannu kan takardun bada shaida ga tubabbun masu aikata laifuka.

DIG Isyaku Mohammed ya ce wasu sarakuna da DPOs kan bayar da shaidar ɗabi’a ga wasu mutane, amma ya ce bai kamata a ba mutanen da suka taɓa aikata manyan laifuka damar shiga aikin tsaro da sunan cewa sun tuba ba.

Ya bayyana cewa ya taɓa aiki a yankin Arewa maso Gabas, inda sojoji suka karɓi wasu tubabbun mayaƙan Boko Haram, suka yi musu gyaran hali tare da sake mayar da su cikin al’umma.

A cewarsa, yayin wani taron gari da aka gudanar a Jihar Yobe lokacin da yake jami’in ayyuka, an wayar wa jama’a kai kan su karɓi tubabbun mayaƙan saboda sun tuba, amma al’ummar yankin suka ƙi amincewa da hakan.

Ya ce wasu daga cikin mutanen sun bayyana cewa ba za su iya ganin wanda ya kashe iyayensu ko ya lalata musu dukiya ya dawo cikin al’umma yana samun tallafi ba, alhali waɗanda ya cutar suna nan cikin wahala ba tare da taimako ba.

Sai dai DIG ɗin ya ce batun sake haɗa tubabbun mayaƙa cikin al’umma shawara ce ta gwamnatin tarayya, kuma rundunar ‘yan sanda ba za ta iya hana hakan ba.

Amma ya jaddada cewa abin da rundunar za ta yi shi ne tabbatar da cewa irin waɗannan mutane ba su samu shiga aikin ɗan sanda ba.

Ya ce rundunar na yin duk mai yiwuwa wajen hana ba tubabbun masu laifi kaɗai ba, har ma da sauran bata-gari shiga aikin ‘yan sanda.

DIG Isyaku Mohammed ya kuma buƙaci shugabannin al’umma su riƙa tona asirin masu laifi maimakon ba su goyon baya, yana mai cewa idan aka taimaka musu suka shiga aikin tsaro, daga baya za a iya mayar da su yankunan da suka fito domin su yi aikin ‘yan sanda.

Ya ƙara da cewa rundunar za ta ƙaddamar da sintirin haɗin gwiwa a iyakokin Jihar Kwara domin yaƙi da masu aikata laifuka.

“Kwara na da iyaka da jihohin Ekiti da Oyo da Kogi da Neja tare da ƙasar Benin, saboda haka za a ƙarfafa sintiri a kan iyakokin domin hana shigowa da ayyukan ta’addanci da sauran laifuka”

DIG ɗin ya kuma bayyana cewa Sufeto Janar na ‘Yan Sanda ya umarci dukkan DIGs su zagaya jihohin da ke yankunansu domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki, gano matsalolin tsaro kai tsaye tare da nemo hanyoyin magance su.

Haka kuma ya yi kira da a rungumi tsarin tsaron al’umma, yana mai cewa tsarin yana bai wa jama’a damar mallakar dabarun kare yankunansu.

Ya kuma jaddada muhimmancin bayar da bayanan sirri cikin gaggawa ga jami’an tsaro tare da ƙarfafa matasa su shiga ayyukan da za su amfani al’umma.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata