DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeLabaraiAn naɗa Dakta Lawan Ahmed a matsayin sabon sarkin Gumel

An naɗa Dakta Lawan Ahmed a matsayin sabon sarkin Gumel

Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi, ya amince da naɗin Dakta Lawan Ahmed Muhammad Sani a matsayin sabon sarkin masarautar Gumel na 17, domin maye gurbin mahaifinsa da ya rasu kwanan nan.

Sakataren gwamnatin jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a madadin gwamnatin jihar a ranar Lahadi, inda ya bayyana cewa amincewar ta biyo bayan shawarar da majalisar masu zaɓen sarki ta masarautar Gumel da kuma majalisar sarakunan jihar Jigawa suka miƙa wa gwamnan.

Sabon sarkin na 17 zai gaji mahaifinsa, marigayi Alhaji Dakta Ahmed Muhammad Sani II, wanda ya riga mu gidan gaskiya a ranar Alhamis, 3 ga watan Satumban 2026, bayan kwashe shekaru 46 yana mulkin masarautar ta Gumel.

Kafin naɗin nasa a matsayin sabon sarkin Gumel, Dakta Lawan Ahmed Muhammad Sani yana riƙe da sarautar Chiroman Gumel, kuma shi ne daraktan tsaron intanet a Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA).

Gwamna Namadi ya nuna godiyarsa ga majalisar masu zaɓen sarkin Gumel a ƙarƙashin jagorancin Wazirin Gumel, Alhaji Adamu Muhammad Nasoro, da kuma sarakunan Hadejia, Kazaure, Ringim, da Dutse da ke cikin majalisar sarakunan jihar kan shawarwarin da suka bayar wajen zaɓen sabon sarkin.

A madadin gwamnatin jihar Jigawa, gwamnan ya taya sabon sarkin murna tare da yi masa fatan samun nasarar gudanar da shugabanci mai albarka ga masarautar Gumel da ƙasa baki ɗaya.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata