DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeLabaraiSabbin masu rajistar zaɓe sun haura miliyan 6.8 gabanin zaɓen 2027

Sabbin masu rajistar zaɓe sun haura miliyan 6.8 gabanin zaɓen 2027

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ce ta yi wa sabbin masu zaɓe 6,885,330 rajista a matakai uku na shirin ci gaba da rajistar masu zaɓe (CVR) domin babban zaɓen shekarar 2027. An tsawaita wa’adin rajistar zuwa ranar 26 ga Yulin 2026, bayan da aka fara tsara rufewa a ranar 10 ga Yuli.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito, ta nakalto shugaban kwamitin wayar da kan masu zaɓe na INEC, Mohammed Kudu Haruna, yana cewa za a wallafa rijistar masu zaɓe domin karɓar ƙorafe-ƙorafe da gyare-gyare bayan an kammala tantance bayanan. Har ila yau, wani jami’in INEC da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa hukumar na sa ran tace rijistar kafin ta fitar da adadin ƙarshe.

Daga cikin sabbin masu rajistar, 3,631,488 sun yi rajista ta yanar gizo, yayin da 3,253,842 aka yi musu rajista kai tsaye.

Mata sun kai kashi 52.57% na masu rajista, yayin da matasa masu shekaru tsakanin 18 zuwa 34 suka fi rinjaye. Haka kuma, ɗalibai ne suka fi yawa a cikin rukunin masu rajista bisa sana’a.

Binciken ya nuna cewa Arewa maso Yamma ce ta fi yawan sabbin masu rajista da sama da miliyan 1.56, inda Jihar Kano ta zo ta farko da mutum 465,964, sai Sakkwato da 338,730.

Rahoton ya kuma nuna cewa INEC ta dakatar da rajista a wasu jihohi saboda zaɓukan cikin jihohi, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen tantance rijistar domin cire masu rajista sau biyu da bayanan da ba su dace ba.

Masana harkokin siyasa sun ce yawan masu rajista zai amfani dimokuraɗiyyar Nijeriya ne kawai idan aka samu yawan fitowar masu kaɗa ƙuri’a ranar zaɓe. Sun kuma buƙaci INEC da jam’iyyun siyasa su ƙara wayar da kan jama’a kan muhimmancin karɓar katin zaɓe da shiga zaɓe.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata