DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeLabarai'Dole Afirka ta daina fitar da albarkatun ƙasa ba tare da sarrafawa...

‘Dole Afirka ta daina fitar da albarkatun ƙasa ba tare da sarrafawa ba’

Mataimakin Shugaban Nijeriya, Sanata Kashim Shettima, ya ce lokaci ya yi da ƙasashen Afirka za su daina fitar da albarkatun ƙasa ba tare da sarrafa su ba, tare da mayar da hankali kan gina masana’antu da za su ƙara musu ƙima domin samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziƙi.

Kamfanin Dillancin Labarai na NAN ya ruwaito cewa Shettima ya bayyana haka ne a ranar Juma’a yayin ziyarar duba Glo-Djigbé Industrial Zone (GDIZ) da ke birnin Cotonou na Jamhuriyar Benin. Ya ce ziyarar na daga cikin umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin koyon ingantattun dabarun bunƙasa masana’antu.

Shettima ya nuna takaicinsa kan yadda Afirka ke cin moriyar kusan kashi ɗaya cikin ɗari ne kawai na masana’antar auduga ta duniya mai darajar dala biliyan 370.

Ya ce farfaɗo da sarkar sarrafa auduga a Nijeriya zai samar da miliyoyin ayyukan yi, ƙara kuɗaɗen shiga daga kayayyakin da ake fitarwa da kuma bunƙasa tattalin arziƙi.

Ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya na shirin kafa yankunan masana’antun noma guda takwas a jihohi takwas, tare da kwaikwayon tsarin da Benin ta yi na haɗa noma da masana’antu wajen sarrafa auduga, goro da waken soya zuwa kayayyakin da aka sarrafa.

Shettima ya samu rakiyar gwamnonin jihohin Kwara, Imo, Katsina, Filato, Zamfara da Jigawa yayin ziyarar, inda suka duba masana’antun sarrafa auduga, goro da sauran amfanin gona domin samun darussa da za a aiwatar a Nijeriya.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata