DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeSiyasa'Yan majalisar adawa sun bukaci Tinubu ya saki El-Rufai

‘Yan majalisar adawa sun bukaci Tinubu ya saki El-Rufai

‘Yan majalisar adawa a majalisar wakilai sun bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dauki matakan gaggawa da tsaurara wajen kawo karshen ta’addanci, ‘yan bindiga, kashe-kashe da garkuwa da mutane da ke ci gaba da addabar wasu sassan arewacin Nijeriya.

‘Yan majalisar sun kuma bukaci gwamnatin tarayya ta saki tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda suka ce ci gaba da tsare shi na kara nuna abin da suka kira “matsin lamba ga abokin hamayyar siyasa”.

A cikin wata sanarwa da shugaban ‘yan majalisar adawa, Fredrick Agbedi, da kakakinsu, Afam Ogene, suka sanya wa hannu ranar Alhamis, sun ce yawan hare-haren da ake kai wa ya wuce misali, inda ake kashe ‘yan Nijeriya a gidaje, gonaki da al’ummominsu, yayin da wasu ke yin garkuwa da su a lokacin ibada.

‘Yan majalisar sun bukaci Shugaba Tinubu ya kaddamar da wani gagarumin farmakin soji mai dorewa, wanda zai dogara da sahihan bayanan sirri, domin kwato al’ummomi da dazuzzukan da ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga da sauran kungiyoyin masu aikata laifuka suka mamaye.

Sun kuma bukaci gwamnati ta yi la’akari da ware dala biliyan biyar daga kudaden ajiyar kasashen waje domin gudanar da wani gagarumin shirin musamman na inganta tsaron kasa.

Dangane da Nasir El-Rufai, ‘yan majalisar sun ce ci gaba da tsare tsohon gwamnan na jawo tambayoyi kan yadda gwamnatin tarayya ke aiwatar da yaki da cin hanci da rashawa.

Sun ce ya kamata yaki da cin hanci ya kasance yaki da cin hanci, ba hanyar yakar abokan hamayyar siyasa ba. Saboda haka suka bayyana El-Rufai a matsayin “fursunan siyasa”, tare da bukatar a sake shi nan take.

‘Yan majalisar sun kuma yi tambaya kan daidaiton yadda ake aiwatar da yaki da cin hanci, inda suka yi nuni da wasu mutanen da suka samu mukamai a yakin neman zaben jam’iyyar APC, duk da zargin cin hanci da rashawa da suka taba fuskanta.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata