Akalla mutane 633 ne suka mutu yayin da kusan 3,000 suka bace sakamakon wata mummunar ambaliyar ruwa da laka da ta afku a yankunan Nepal da Tibet na ƙasar China.
Rahoton jaridar Punch, wanda ya dogara da rahotannin hukumomi da kamfanin dillancin labarai na AFP, ya ce ambaliyar ta afku ne bayan wani mamakon ruwa, kankara, laka da tarkace sun kwarara tare da ratsawa a yankunan Himalaya da kuma mamaye kauyuka.
Nepal mutane 626 ne aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da mutane 2,426 suka ci gaba da kasancewa cikin wadanda ba a san inda suke ba. A Tibet kuma, mutane bakwai sun mutu yayin da 554 suka bace, a cewar hukumomin China.
Hukumomin Nepal sun kara da ma’aikatan tashoshin samar da wutar lantarki 933 cikin jerin wadanda suka bace. Haka kuma, wasu daga cikin wadanda ake nema sun hada da masu yawon bude ido da mahajjatan da ke kan hanyarsu zuwa Dutsen Kailash da ke Tibet.
A cewar kungiyar Red Cross, kimanin mutane 93,000 ne lamarin ya shafa, yayin da ake ci gaba da fargabar sake samun ambaliyar ruwa a wasu wuraren saboda samuwar manyan tafkuna sakamakon laka da kankara.
Jami’an ceto a Nepal sun kuma gano wasu mutane da suka makale a cikin wani rami na aikin samar da wutar lantarki na Trishuli 3A. Kimanin mutane 350 da suka makale a wurin an ceto su, yayin da ake ci gaba da kokarin ceto wasu sama da 100.
A bangaren Tibet, hukumomin China sun dakatar da wasu ayyukan ceto a yankin Gyirong saboda fargabar sake samun ambaliyar ruwa, kafin daga bisani su ce barazanar ta ragu. An kuma ceto wasu mazauna yankin biyu.
A Indiya kuma, hukumomi sun ce an gano gawarwaki bakwai a cikin kogunan da ke kwarara daga Nepal, wadanda ake kyautata zaton wadanda ambaliyar ta rutsa da su ne.
Rahotannin baya-bayan nan daga Reuters sun tabbatar da cewa ambaliyar, wadda ta samo asali daga rugujewar kankara a yankin Himalaya, ta kashe akalla mutane 626 a Nepal da bakwai a Tibet, yayin da kusan mutane 3,000 ke ci gaba da bacewa.
