DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeSiyasaObasanjo da Obi sun nemi sauya tsarin dimokuraɗiyya a Nijeriya

Obasanjo da Obi sun nemi sauya tsarin dimokuraɗiyya a Nijeriya

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, da ɗan takarar shugaban ƙasa na Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, sun yi kira da a yi gagarumin sauyi a tsarin dimokuraɗiyya da hukumomin siyasa a Nijeriya.

Sun bayyana hakan ne a ranar Talata a wajen taron tattaunawa kan dimokuraɗiyya na Goodluck Jonathan Foundation na shekarar 2026, wanda aka gudanar a Bauchi, babban birnin Jihar Bauchi.

Punch ta ruwaito cewa taron, mai taken “Beyond Elections: Can Political Parties and the Judiciary Save African Democracy?”, ya tattauna kan rawar jam’iyyun siyasa da bangaren shari’a wajen kare dimokuraɗiyya a Afirka.

Obasanjo, wanda ya jagoranci taron, ya ce tsarin dimokuraɗiyyar da ƙasashen Afirka suka gada daga ƙasashen Yamma bai yi la’akari sosai da tarihi, al’adu da ƙimar Afirka ba.

Ya ce tsarin zaɓe na “wanda ya yi nasara ya mallaki komai” yana ƙara rura rikicin siyasa, inda abokan hamayya ke kallon juna a matsayin maƙiya maimakon abokan tafiya wajen tafiyar da ƙasa.

“Dimokuraɗiyyar da muke aiwatarwa ba ta da mahalli a Afirka, ba ta da abin da ya shafi Afirka,” in ji Obasanjo.

Tsohon shugaban ya kuma ce bambancin al’ummomin Nijeriya muhimmin ginshiƙi ne na ƙasar, yana mai gargadin cewa bai kamata a yi watsi da shi ba wajen tsara tsarin mulki da dimokuraɗiyya.

Ya kuma nuna damuwa kan yadda kuɗi da sayen kuri’u ke ƙara yin tasiri a siyasar Nijeriya, tare da ƙarancin wakilcin mata a manyan mukaman siyasa.

A nasa ɓangaren, Peter Obi ya zargi wasu masana, ’yan majalisa, lauyoyi, shugabannin addini da wasu jami’an shari’a da taimakawa wajen raunana hukumomin dimokuraɗiyya a Nijeriya.

Obi ya ce wasu sauye-sauyen da aka yi wa dokokin zaɓe da kuma yadda ake tafiyar da wasu shari’o’in zaɓe na nuna cewa tsarin dimokuraɗiyyar ƙasar na fuskantar babbar matsala.

Ya ce, “Inda ’yan majalisa suka cire magudin takardu daga cikin laifukan da suka shafi zaɓe, sannan manyan lauyoyi suna kare waɗanda ake zargi da yin jabun takardu. Shugabannin addininmu kuma suna yi wa ’yan siyasar da ake zargi da aikata laifi addu’ar samun albarka. Muna cikin rikici.”

Obi ya kuma soki bangaren shari’a, yana zargin cewa wasu alkalai sun fara nuna kusanci da siyasa.

A yayin taron, shugabar Jjam’iyyar Labour Party, Nenadi Usman, ta yi kira ga ’yan siyasar da ke shirin shiga zaɓen 2027 da su yi koyi da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, wanda ta ce ya nuna kishin ƙasa lokacin da ya amince da shan kaye a zaɓen shugaban ƙasa na 2015.

Nenadi Usman ta ce Nijeriya ta tsallake rikicin da ake hasashen zai biyo bayan zaɓen 2015 ne saboda Jonathan ya amince da sakamakon zaɓen kafin ma a kammala tattara dukkan ƙuri’un.

Taron ya samu halartar tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Namadi Sambo, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, da sauran manyan ’yan siyasa, masana tsarin mulki da wakilan ƙungiyoyin farar hula.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata