DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeKetareTrump ya tabbatar da sauya masa jirgi a asirce saboda barazanar Iran

Trump ya tabbatar da sauya masa jirgi a asirce saboda barazanar Iran

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya amince cewa jami’an tsaron Amurka sun sauya jirgin da ya yi amfani da shi wajen barin Turkiyya a asirce saboda fargabar wata barazana daga Iran.

Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai, bayan rahotanni sun ce an sauya shi daga jirgin Air Force One zuwa wani ƙaramin jirgin soji yayin dawowarsa daga taron ƙungiyar NATO da aka gudanar a Ankara.

Rahoton Premium Times ya ce an sauya jirgin Trump ne a ranar 8 ga Yuli, bayan ya halarci taron NATO a Ankara. Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun yi imanin cewa akwai wata barazana daga wasu ƙungiyoyin da ke da alaƙa da Iran.

Trump ya ce jami’an rundunar sojin Amurka da jami’an tsaron fadar White House ne suka umarce shi da ya shiga wani jirgi daban.

“Na bi shawarar jami’an sirri da sojoji. Sun so in shiga wani jirgin daban. Ina tsammanin akwai wata barazana, amma ban tambayi cikakken bayani ba,” in ji Trump.

Rahotanni sun ce Trump ya fara shiga tsohon jirgin Air Force One a idon manema labarai, amma daga baya aka fitar da shi a asirce zuwa wani jirgin soji kirar C-32A, wanda ya kai shi Birtaniya domin shan man fetur.

Manema labaran da ke tafiya tare da shugaban Amurka ba su san cewa Trump ya sauya jirgi ba, inda su kuma suka ci gaba da tafiya a cikin tsohon Air Force One da ake ganin kamar shugaban yana ciki.

Rahotanni sun ce an kuma umarci manema labaran da ke cikin jirgin da su rufe tagogin jirgin yayin tafiyar daga Turkiyya zuwa Birtaniya, matakin da ya ƙara haifar da tambayoyi kan dalilin sauyin jirgin.

Bayan isa Birtaniya, Trump ya koma tsohon Air Force One kafin daga bisani ya sake shiga sabon jirgin da Qatar ta bai wa Amurka domin ci gaba da tafiya zuwa Washington.

Sauyin jirgin ya faru ne a lokacin da ake fama da tsananin rikici tsakanin Amurka da Iran. Wasu rahotanni sun ce jami’an Amurka sun samu bayanan sirri kan wata barazana da ake zargin wakilan Iran za su kai wa Trump.

Sai dai Trump ya ce barazanar da ake yi masa ba sabon abu ba ce, yana mai cewa shugabannin Amurka suna fuskantar barazana akai-akai.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata