DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 29, 2026
HomeLabarai'An samu raguwar cin zarafin mata a Nijeriya da kaso 81'

‘An samu raguwar cin zarafin mata a Nijeriya da kaso 81’

Hukumar Kare Haƙƙin Dan Adam ta Ƙasa (NHRC) ta bayyana cewa an samu raguwar kaso 81 cikin 100 na rahotannin cin zarafi da wariya da ake yi wa mata a Nijeriya tsakanin watan Afrilun 2025 da Afrilun 2026.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, alkaluman hukumar sun nuna cewa yawan korafe-korafen ya sauka daga 11,667 a Afrilun 2025 zuwa 2,212 a Afrilun 2026. Lamarin ya haɗa da cin zarafin mata, auren dole, cin zarafin haƙƙin haihuwa, hana mata ganin ‘ya’yansu, safarar mutane da kuma wasu al’adu masu cutarwa ga mata.

Duk da wannan ci gaba, masu fafutukar kare haƙƙin mata sun yi gargadin cewa har yanzu akwai mata da dama da ba sa kai rahoton cin zarafin da ake yi musu saboda tsoro, kunya ko rashin samun adalci.

Bayanan sun nuna cewa rahotannin wariyar jinsi sun ragu daga 1,739 zuwa 752, yayin da al’adu masu cutarwa suka sauka daga 1,571 zuwa 79. Haka kuma auren dole ya ragu daga 1,608 zuwa 96, yayin da safarar mata da yara mata ta sauka daga 1,560 zuwa 187 a cikin shekarar.

Ministar Harkokin Mata da Ci Gaban Jama’a, Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim, ta ce har yanzu miliyoyin yara mata na fuskantar matsaloli kamar rashin ilimi, auren wuri da cin zarafi. Ta jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da ɗaukar matakan kare mata da yara mata tare da tabbatar da mutuncinsu da walwalarsu.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata